- Marubuci, Armand Mouko Boudombo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journaliste -BBC Afrique
- Twitter,
El hadj Souleymana, mai shekara 48 a duniya na cikin 54 da suka rasu yayin da ruwa ya yi awon-gaba da motar da suke tafiya a ciki.
Ya bar iyalansa cikin hali na rashin tabbas kasancewar a yanzu haka ba su da wani abin dogaro.
An kwashe tsawon kwanaki muna neman shawo kan Elhadji Ibrahima Ousseni ya tattauna da mu. Yana cikin kaɗuwa ta rashin ɗan’uwansa wanda ya kasance “ginshiƙi a cikin iyalin”.
Ƙanensa El Hadj ya kasance ɗan kasuwa ne wanda ke gudanar da harkokinsa tsakanin birnin Tahoua da kasuwanni masu maƙwaftaka.
“Tun yana yaro, ya kasance mutum mai natsuwa. Haka Allah Ya halicce shi,” in ji Elhadj Ibrahima.
Ibrahima ya ƙara da cewa a lokacin da marigayin ya shekara 48 da haihuwa, ya riga ya ƙulla hulɗar cinikayya da amintaka tsakaninsa da mutane da dama a faɗin ƙasar Hausa.
“Yana da mutane sosai, ta yadda a lokacin aurensa abokansa daga wurare da dama na faɗin Nijar har da Najeriya, kamar Illela da kuma Sokoto sun zo.”
Hanyar da ya saba bi ce a yanzu ta zamo ajalinsa. Shi mazaunin Tahoua ne amma ya shafe gomman shekaru yana zirga-zirga zuwa kasuwanni a Telemces, mai nisan kilomita 120 domin cin kasuwa.
Ashe wannan karon tafiya ce da ba zai dawo ba. Ya zata tafiya ce kamar yadda ya saba, amma bayan tafiyar kimanin kilomita 70 sai suka gamu da kogin Kori ya tumbatsa.
A lokacin rani wannan yanki na kogin na ƙafewa ya zamto babu ruwa.
Wannan yanki na Kogin Kwara ya cika maƙil ne bayan ruwan sama da aka shafe kwana biyu ana zabgawa, kamar yadda Elhadji Sanoussi, ɗaya daga cikin masu zaman makokin ya shaida wa BBC.
Ruwan ya yi awon-gaba da motocin safa biyu, waɗanda ke ɗauke da gomman mutane; 54 daga cikinsu sun mutu, kamar yadda hukumomi suka tabbatar, sannan kuma akwai wasu mutanen da a gano su ba.
Sai washegari ne iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su suka samu labarin.
“Mun je wurin inda muka iske waɗanda suka tsira sun mammaƙale a kan bishiyoyi, a haka suka kwana. Su ne muka ceto. Su ne waɗanda suka kira ƴan’uwansu suka shaida musu abin da ya faru,” in ji Sanoussi Mahamadou.
Marayu 12
Sai dai El Hadj Souleymana ba ya cikin waɗanda Allah ya tseratar; “Lokacin da na ga gawarsa na shiga cikin hali na baƙin ciki,” in ji ɗan’uwan mamacin.
Marigayin ya bar marayu 12 “yawancinsu ƙanana ne” da kuma mata biyu.
Mutuwar El Hadj ta zo ne ana gobe za a koma makaranta, wanda hakan ma ya ƙara jefa iyalin cikin damuwa.
“Wannan babbar matsala ce, muna so hukumomi su taimaka mana. Waɗannan yaran sun zama marayu.
Marigayin mutum ne wanda ake matuƙar girmamawa. “Muna fatan Allah zai kawo mana waɗanda za su taimaka mana.”
Ya kasance mai taimakon al’umma baya ga iyalinsa.
Me gwamnati ta yi?
Yawanci a lokacin da aka samu irin haka, al’umma ne ke haɗuwa suna taimaka wa junansu domin a yi wa waɗanda suka mutu sutura.
“Baya ga ƴan’uwan sauran mamatan, da mu da muka kawo motoci biyar da a-kori-kura shida, ban ga wani jami’in gwamnati ba. Mu ne muka ɗauko waɗanda abin ya rutsa da su. Babu wani shugaba ko hukuma da ta taimaka mana,” in ji Alhadji Sanoussi Mahamadou.
Elhadji Ibrahima kuwa ya ce “ba mu samu taimakon da muka yi tsammani daga hukumomi ba. Domin a lokacin da muke ƙoƙarin tsamo waɗanda suka nutse wata gada ta ɓalle. Amma duk da haka mun ci gaba da aikin ceto har ƙarfe 9 na dare. Babu wani taimako da muka samu.”
Sai dai hukumomin sun bayyana cewa Ministan Jin-ƙai ya bayar da tallafi ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, sai dai bayanin bai tantance ko dukkanin iyalan ne aka taimka mawa ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyra Nijar ya bayyana a ranar 22 ga watan Agusta cewa gwamnatin mulkin soji ta ƙasar ta yanke shawarar amfani da kuɗi biliyan 12 na kuɗin CFA domin magance ambaliyar ruwa.
Jamhuriyra Nijar na fuskantar ambaliyar ruwa a shekarun baya-bayan nan, musamman saboda yanayi na damina wanda bai yin tsawo sai dai kuma ana samun ruwan sama mai ƙarfi.
Ruwan sama a lokacin damina kan sanya Kogin Kwara ya tumbatsa yayin da yakan ƙafe a lokacin rani.
Sai dai masana sun ce wani abu da ke ƙara ta’azzra ambaliyar ruwa a ƙasar ta Nijar shi ne rashin kyakkyawan tsarin birane inda ake yin gine-gine kan hanyoyin ruwa.
Haka nan ma yanayin ƙasar na ƙara munin lamarin, kasancewar ba ta iya tsotse ruwan yadda ya kamata.
A cikin shekara biyu da suka gabata ambaliyar ruwa a Nijar ta yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama. A wannan shekarar kaɗai aƙalla mutum 217 sun riga mu gidan gaskia, kamar yadda hukumomi suka bayyana a cikin watan Agusta.
A cikin mutanen da suka mutu, 108 sun nutse ne a ruwa yayin da gini ya kashe mutum 109.