- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
Hausawa mutane ne da suka yaɗu a wurare da dama na duniya, kuma suna daga cikin al’umma mafiya yawa a nahiyar Afirka.
Mafi yawa daga cikin al’ummar ta Hausa na rayuwa ne a arewacin Najeriya zuwa kudancin Jamhuriyar Nijar. Sai kuma ƙasar Kamaru da Ghana da kuma sauran ƙasashen yammacin nahiyar Afirka.
Sai dai wani fage da ake kai kai-komo a kai shi ne asalin al’ummar ta Hausawa.
Akwai ra’ayi da dama kan hakan, kuma ɗaya daga cikin waɗannan ra’ayoyi da ya fi shahara shi ne batun Bayajida, a matsayin asalin Bahaushe.
BBC ta tuntuɓi Farfesa Ibrahim Malumfashi, masanin adabi da tarihin Hausawa, inda ya fayyace tare da raba aya da tsakuwa a kan tarihin Bahaushe.
A cewarsa, “Babu al’umma da ta faɗo daga sama. Babu al’umma da za ka ce ba halastacciyar al’umma ba ce tun daga zamanin Annabi Adamu. Saboda haka ana bin cikin tarihi ne a duba yadda al’umma na duniya suka samu, da kuma yadda suka wanzu, suka barbazu a doron ƙasa. Dukkanmu muna da yaƙinin asalinmu daga Annabi Adamu ne da Hauwa’u.
Asalin Bahaushe na yanzu
Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce asali mutane ba irin siffar da ake yanzu suke da ita ba.
A cewarsa Hausawa sun kasance daga cikin mutanen da suka tsira daga ruwan da aka tafka a lokacin annabi Nuhu, cikin mutanen da ake kira Omo-Kibishi.
Inda ya ce daga cikin waɗannan al’umma ne al’ummar Hausawa ta samo asali shekara dubu 150 da suka gabata.
“Al’ummar Hausawa kamar yadda tarihi ya nuna sun bar wannan yankin (Habasha) suka gangara zuwa yankin Kogin Chadi daga nan suka shiga Arewacin Afirka. Sai suka koma yankin Larabawa, nan ma sun yi rayuwa ta tsawon lokaci, suka bar wasu iyalai a wajen, suka tafi Asiya, yankin da ake kira Malesiya. Nan ne asalin Hausawa na ƙarshe.”
Ya ce bayan shekara 60,000 suka bar wannan yanki na Malesiya, sai suka sake bin hanyar da suka bi ta farko, inda suka iske ƴan’uwansu da suka rabu shekara da shekaru sun zama ƴan kasa a wuraren. “Sai suka sake zagayowa suka dawo yankin Masar da Falasɗinu da Aljeriya da Maroko da Mauritaniya na yanzu, nan suka zauna na shekaru.
“Idan ka je irin wuraren nan na Maroko da Mauritaniya da Masar da Sudan, wannan yankin baki ɗaya ƴan’uwan Huasawa ne. A wannan lokaci ba da harshen Hausa suke amfani ba, suna amfani ne da harshen mutanen wajen.”
A game da amfani da harshen Hausa na yau, Farfesa Malumfashi ya ce, “ba abu ne da za ka ce ya kai shekara miliyan ɗaya ko biyu ba. Sabo ne, amma masu magana da shi sun daɗe a doron ƙasa.”
Bayajidda a ƙasar Hausa
Tarihin zuwan wani mutum da ake kira Bayajida ƙasar Hausa na daga cikin mafi shahara idan ana batun asalin Bahaushe.
Farfesa Malumfashi ya ce: “Saboda daɗewa na tarihi, abin da Hausawa suke iya tunawa shi ne maganar Bayajidda. Shi tarihi na Bayajidda sabon abu ne, bai kai shekarun da muka yi magana a kai ba.
Farfesan ya ce maganar Bayajida tarihihi (tarihin da ba na gaskiya ba) ne. “Abu ne wanda ya faru, amma an juya shi wanda idan ba ka tsaya ka tantance shi ba, za ka ɗauke shi a matsayin gaskiya, alhali akwai gaskiya akwai labaran da ba gaskiya ba,” in ji Malumfashi.
“Bayajida da ake magana wanda ake cewa Abu Yazid, wanda aka ce mutumin Bagadaza ne, ɗan Sarkin Bagadaza Abdullahi, a cikin tarihi ba a yi shi ba. Wanda aka yi, wanda kuma ake tsammanin ya zo ƙasar Hausa, mutum ne wanda ya taso daga ƙasar Tunisia mahaifinsa kuma zaunannen yankin yammacin Afirka ne wanda ya zauna a kusa da ƙasar Timbuktu.
“Daga baya ya koma Tunisia, a nan ya zauna ya yi kasuwanci a nan ya zauna ya zama babban malami ya zama mayaƙi. Daga baya aka kama shi, aka tsire shi, dabbobin daji suka cinye shi.
“Ƴaƴansa da dakarunsa suka bar wannan yanki na Tunisia suka gangaro yankin Daular Borno ta yanzu. A nan cikin wannan daular ce ko dai ƴaƴansa ko cikin dakarunsa ko jikokinsa wani daga cikinsu ya auri ƴar Mai na Borno, shi kuma Mai na Borno ya nemi ya kashe shi, sai ya gudu da wannan mata, suka isa ƙasar Daura. Saboda haka ba asalin Bayajiddan ba ne ya zo ƙasar Hausa, daga cikin dakarunsa ko ƴaƴa ko jikokinsa ne.”
Zuwan Hausa Arewacin Najeriya
Farfesa Malumfashi ya ce bayan Hausawa sun bar yankin Maroko da Masar da Aljeriya, suka gangaro zuwa bakin Tekun Chadi.
“Nan Hausawa suka zauna kafin shigowa ƙasar Hausa. A zaman wajen ne aka samar da kakan harshen hausa na asali, wato harshe ɗan ahalin Afirka da Asiya. Wato Afroasiatic, shi wannan ne ya haifar da harsuna aƙalla biyar ciki har da ahalin chardiac.
“Hausa suna cikin ƴaƴa bakwai na wannan ahali. Bushewar wannan kogin ta sa mutane suka taso suka koma yankin da ake kira ƙasashen Hausa a yanzu musamman Nijar da Arewacin Najeriya.”
Malam Malumfashi ya ce yanayin zirga-zirga da mutane suka riƙa yi, ya sa sun yi addinai da dama, wanda hakan ya sa a cewarsa Hausawa ba Musulmi ba ne kawai.
“Misali, muna yara muna wata waƙa da ake cewa ‘Rana buɗe, rana buɗe in yanka miki ragon sarki, ki sha jini shar-shar. Wannan na nuna Hausawa sun yi bautar rana. Kuma inda aka yi bautar rana guda biyu ne: yankin Asiya da Hausawa suka baro da yankin Arewacin Afirka musamman Falasɗinu da Masar.”