Asalin hoton: ORTN

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta gabatar da wani ƙudiri na yanke wani kaso na albashin ma’aikatan ƙasar domin yin wani asusu na musamman domin samun kudaden gudanar da wasu ayyukan gwamnati.

Manufar asusun shi ne tattara kuɗaɗe daga al’ummar ƙasar domin tallafa wa ayyukan gwamnati, musamman fannin tsaro da sauran muhimman ɓangarori da ke fuskantar gazawa da taɓarɓarewa tattalin arziki tun bayan juyin mulkin 2023.

Wannan batu ya janyo zazzafar muhawara a ƙasar musamman tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago, waɗanda ke ganin matakin a matsayin wata hanya ta tatsar ma’aikatan.

A baya-bayan nan dai hukumomin asusun suka sha caccaka a shafukan sada zumunta bayan wasu bayanai da shugaban asusun ya fitar kan kuɗaɗen da ya ce asusun ya ce ya kashe, ciki har da amfani da intanet, ta kimanin saifa miliyan 45 a ofishin gidauniyar cikin wata shida.

Me ƙungiyoyin ma’aikatan ke cewa?

Ƙungyoyin ƙwadagon ƙasar na ɓangarori daban-daban suna nuna rashin jin daɗinsu game da wannan yunƙuri.

Tun da farko uwar ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ce ta aike wa ɓangarorin ƙungiyar da wasiƙa in da a ciki ta nemi ra’ayinsu dangane da sabuwar buƙatar gwamnatin mulkin sojin ƙasar.

To sai dai cikin wani martani da ƙungiyoyin suka aike wa uwar ƙungiyar tasu sun ce sun yi watsi da wannan buƙata.

Kungiyar malaman makaranta da SENAN na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwadagon da suka riga suka yi fatali da wannan ƙuduri tare da ƙin amincewa da duk wata hanya da za a yanke wa mambobinta albashi.

Mataimakin sakataren ƙungiyar na farko Gali Dauda ya shaida wa BBC cewa ƙungiyarsu ba za ta bayar da ƙofar yanke wa mambobinta albashi ba.

”Ba mu gamsu da wanna matakai ba, saboda bbau wta huja da ke nuna cewa kuɗaɗen da za a yanken za su kai inda ake buƙata ba, kan haka ne muka ɗauki matakin kin amincewa da wannan ƙudiri”, a cewarsa.

A nata ɓangare gamayyar ungiyar ƙwadago ta SNT ta malaman sakandire ta ce har yanzu ba ta kai ga ɗaukar matsayi kan ƙudirin ba.

Sakataren ƙungiyar Jariri Labbo ya ce duk da cewa ƙungiyar ba ta zauna kan batun ba, amma bai nuna alamun amincewa da matakin ba.

”A daidai lokacin da ƴan kwantiragi ke jiran a ɗauke su aiki, kuma daidai lokacin da ma’aikata ke buƙatar ƙarin albashi, kuma sai a fito da wani batu na yanke musu alashi?, kuma sai a ce su ne za a tambaya su bai wa gwamnatin kuɗi”, a cewarsa.

Ita kuwa haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwadago na USPT ta bakin jami’inta Sale Brahima, ya ce suna ci gaba da tuntuɓar juna a asirce domin ɗaukar mataki kan batun.

Nijar na cikin halin rashin kuɗi – Masana

ma'adinin Uranium
Asalin hoton: Getty Images, Nijar na da ɗimbin arzikin ma’adinin Uranium

Dakta Abba Sadiq mai sharhi kan harkokin siyasar ƙasashe kuma malami a jami’ar Canada, ya ce matakain bai zo musu da mamaki ba la’akari da ƙarancin kudi da ƙasar ke ciki.

”Babban Nijar fa shi ne ma’adinin Uranium, wanda kuma yanzu ba a iya fitar da shi tun da an rufe iyakar ƙasar da Benin balle a sayar da shi a samu kuɗi”, in ji shi.

Masanin ya ara da cewa arzikin ƙasar na biyu shi ne man fetur, wanda a cewarsa shi ma ba a iya fitar da shi.

”Wannan hali ne ya jefa ƙasar cikin halin rashin kuɗi kuma take neman hanyar da za ta samu kuɗaɗe domin gudanarwa”, kamar yadda ya bayyana.

Masanin ya ƙara da cewa dama a baya ƙasashen Turai na tallafa wa ƙasar da kuɗaɗe, to amma sakamakon juyin mulkin ƙasar duka waɗannan tallafi sun tsaya, don haka dole ta sa gwamnati ta lalubo wasu hanyoyin domin riƙe kanta.

”Don haka a iya cewa Nijar na cikin lalurar kuɗi, in ma ba a ce ta talauce gaba ɗaya ba, don haka dole sai ta yi nazarin sake samo wata hanyar sama mata kuɗi,” in ji shi.

‘Dole sai ma’aikatan sun yarda’

Malamn Jami’ar ya ce da ake dole sai ma’aikatan sun yarda, ba za a yi musu dole ba matakin ka iya gamuwa da cikas.

”Dole ta sa ma’aikatan za su yi watsi da ƙudirin saboda, albashin ba yawa ba ne da shi, kuma za ka samu fiye da mutum 10 na dogara kan albashin mutum guda, don yake idan aka rage wa ma’aikaci guda albashi, batun zai shafi a’umma da dama”, a in ji shi.

”A Doka dole sai ma’aikatan sun amince sannan a cire albashin nasu, babau inda doka ta bayar da dama a yanke wa ma’aukata albashi ba tare da amincewarsu ba”, a cewarsa.

Ya kuma tun da ƙungiyoyin ƙwadago da dama na ƙasar sun yi watsi da shi, dole ne gwamnatin ta sake nazarin sake duba wata hanyar.

Ko matakin zai rage wa gwamnati farin jini?

Mai sharhi kan al’amuran siyasar ƙasashen ya ce matakin zai iya raunana farin jinin gwamnatin mulkin soji a wajen ma’aikata da ma ƴan ƙasa.

Ya ce a yanzu gwamnatin ta ce idan mutane sun yarda ne, kuma da alama mutanen ba su yarda ba, don haka idan gwamnatin ta ce za ta yi musu dole, to lallai hakan zai shafi martabarta.

”Sojojin sun ce sun yi juyin mulki ne kan yadda ƴansiyasa ke tafiyar da arzikin ƙasar da yadda alaƙar ƙasar da ƙasashen waje kamar Faransa yadda ta ce ana cutar da ƙasar, kan haka ne ƴan ƙasa ke goyon bayansu, to yanzu idan suka ce za su yanke wa ma’aikata kuɗi ta tilas ba shakka mutane za su daina goyon bayan gwamnatin”.

Me ya kamata gwamnati ta yi don samun kuɗi?

Malamin jami’ar ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi, shi ne ta ƙwato kuɗaɗen da ta yi ikirarin wasu ƴansiyasa sun sace.

”Mutanen da aka ce sun sace kuɗin gwamnatinfa a cikin ƙasar suke, kuma an san inda suke, to ya kamata abi su a karɓo kuɗaɗen da suka sata, domin amfanin gwamnati”, in ji shi.

Sai dai kuma ya ce da alama gwamnatin mulkin sojin ba ta mayar da hankali kan wannan ɓangare ba.

‘Akwai mutanen da suka sace dukiyar gwamnati, kuma an tabbatar da hakan, to ya kamata a je a karɓosu.

Sannan Malamin Jama’a ya ce ya kamata gwamnati ta rage kashe kuɗaɗe ta hanyar rage hadiman manyan jami’an gwamnati.

”Mutu guda sai ya ɗauki hadimai fiye da 20 waɗanda dole sai an biya su albashi, idan kowane jami’i ya rage yawan hadimai da rayuwar facaka, to lallai za a samu kuɗin da za a ririta gwamnati”, kamar yadda ya bayyana.

By Ibrahim