Gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagoranci Abdourrahmane Tchiani ta yi garambawul ga dokar tsarin aikin yi wa ƙasa hidima.
A cikin wata takarda da shugaban majalisar mulkin ta CNSP ya saka wa hannu, gwamnatin ta ce ta dawo da matakin tilasta bai wa ‘yan bautar ƙasa horon aikin soja na tsawon kwanakin 45 daga cikin wa’adin shekaru biyu na aikin yi wa ƙasar hidima.
Takardar ta ƙara da cewa hakan ba zai hana dama ga kamfanoni da ma’aikatu da ba na gwamnati ba da ma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa samun masu bautar ƙasar a lokacin da suke da bukata ba.
Wajibi ne dai ga dukkan mutumin da ya kammala karatun jami’a kuma bai wuce shekaru 30 ba ya yi wa kasa hidima a jamhuriyar ta Nijar domin tunkarar rayuwarsu.
Kuma a shekarun baya dole ne kowane ɗan bautar ƙasa ya samu horon aikin soji a lokacin yi wa ƙasar tasa hidima.
Me ya sa za a yi musu horon soji?
Gwamnatin sojin ta Nijar dai ta ce abin da yake faruwa a aikin yi wa ƙasa hidima tsakanin matasa ya yi karo da ƙudirin ƙasar na tabbatar da cewa matasan sun samu irin gogayyar da suke buƙata wajen tunkarar ƙalubalen da ke gabansu a rayuwa – wanda shi ne maƙasudin yin aikin bautar ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin dai ta yi wa dokar kwaskwarima ne da manufar “cusa wa ƴan ƙasar kishin ƙasa da haɓaka ƙwarewarsu” domin tunkarar rayuwa.
“Mun gano wasu matsaloli da ke faruwa a tsakanin masu yi wa kasar hidima wanda shi ne dalilin da ya sa muka yi wa dokar kwaskwarima.” In ji sanarwar.
Mene ne amfanin horon soji ga ƴan Nijar?
Malam Abbas Abdul’aziz masanin tsaro ne a jamhuriyar Nijar kuma ya ce lallai wannan tsarin da aka dawo da shi yana da muhimmanci sosai ga ƴan ƙasar musamman ma a halin da jamhuriyar ta Nijar ke ciki.
“Idan ka je ka yi kwana 45 ana koya maka harkar aikin soja zai ba ka damar sanin yadda za ka riƙe bindiga da wasu abubuwa masu dama na tsare kai da ƙasa. Sanna idan ta kai ta kawo ana iya ɗaukar su ma a matsayin masu taimakawa lokacin yaƙi.
Kenan shirin yana da amfani guda biyu – na ɗaya zai saka wa jama’a kishin ƙasa sannan na biyu zai bai wa ƙasar damar ƙirƙirar wata runduna ta musamman yadda idan ta ɓaci za a iya nemo waɗanda suka fi ƙwarewa a cikinsu domin kai su fagen daga. Sannan kuma za su samu ƙwarewa wajen gyaran bindiga idan ta lalace.” In ji Abbas Abdu’azeez.