Asalin hoton, Agencies/X
Shugaban mulkin sojin Nijar, Birgediya Janar Abdurrahamane Tchiani, ya zargin Najeriya da Faransa da kitsa yunƙurin afka wa ƙasarsa ko yi wa Nijar bi-ta-da-ƙulli.
A wata hira da ya yi da gidan talbijin na ƙasar, Janar Tchiani ya ce “Faransa ta yi alƙawarin bai wa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wasu kuɗaɗe don kafa sansannin soji a dajin Baga, a jihar Borno”.
“Akwai kuɗin da suka ce za su bai wa Tinubu domin ya ba su wani wuri cikin dajin Baga, wanda Turawan suka yi wa laƙabi da ‘Canada’, inda suke horas da al’umomin yankunan”.
‘Faransa ta ƙulla ƙawance da mayaƙan ISWAP da Boko Haram domin horas da su da ba su makamai da kuɗaɗe domin ta yi amfani da su wajen tayar da zaune-tsaye a Jamhuriyar Nijar”, in ji shi.
‘Faransa na da hannu a Lakurawa’
Asalin hoton, AFP
Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke jihohin Sokoto, Zamfara, da Kebbi.
”Wasu manyan ‘yanta’adda da muka kama sun shaida mana cewa a ranar 4 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, Faransa ta ƙulla wata yarjejeniya da mayaƙan ISWAP, kuma shugabannin Najeriya na sane da ita, cewa za a mayar da dajin Gaba a jihohin Sokoto, Zamfara, da Kebbi a Najeriya sansanin horas da mayaƙan Lakurawa”, in ji shugaban na Nijar.
Janar Tchiani ya yi zargin cewa an tanadi sansanin ne domin horas da mayaƙan Lakura don su watsu a jihohin Sokoto, Zamfara, da jihar Kebbi da kuma jamhuriyar Nijar.
Shugaban na Nijar ya ce duk da iƙirarin mayaƙan da suka kama suka na cewa jagororin Najeriya na sane, ba su yarda da maganar ‘yan bindigar ba.
”Kan haka ne muka yanke shawarar bai wa Najeriya waɗannan bayanai, saboda ba mu yarda da jawaban na ‘yan bindigar ba, muka faɗa wa shugaban hukumar leƙen asiri ta NIA na wancan lokaci da Ahmad Rufai Abubakar, ya turo mutane cikin Nijar domin tattaunawa da ‘yan ta’addar domin tabbatar wa daga bakinsu”.
Amma daga ƙarshe, a cewar shugaban Nijar, sun gwammace ba su faɗa masa wannan sirri ba, inda suka zarge shi da ɗaukar nauyin horas da ‘yan ta’adda.
”Ashe shi wannan Ahmad Rufai Abubakar da muka shaida wa wannan sirri, shi ne ke ɗaukar nauyin tura ‘yanta’adda zuwa wata ƙasa da ake kira Central Africa domin samun horo”, in ji shi.
Haka ma shugaban na Nijar ya zargi mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da masaniya game da wannan batu.
”Duk sun san da zancen, amma suka yi shiru, tun daga nan ne muka fahimci cewa kifi tun ga kai nai ya ruɓe”.
Yayin zargin cewa an ƙuduri aniyar horas da Lakurawan ne domin su kawo tarnaƙi ga aikin bututun man ƙasar da ka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin mai makwabtaka.
Janar Tchiani ya zargi ƙasashe makwabtan Nijar da bayar da taimako ga Faransa domin kafa sansanoni a ƙasashen don horas da ‘yanta’adda da niyyar yaƙar Nijar.
A baya-bayan nan dai, dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar na ci gaba da yin tsami; ko a makon da ya gabata ma gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta zargi Najeriya da shirya mata maƙarƙashiya, kodayake gwamnatin Najeriya ta musanta zargin.
Martanin gwamnatin Najeriya
Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Gwamnatin Najeriya ta musanta duka zarge-zargen na shugaban mulkin sojin na Nijar.
Cikin hirarsa da BBC, ministan yada labaran ƙasar, Mohammed Idris, ya ce Najeriya ba ta taɓa ƙulla wata alaƙar soji da Faransa ko wata ƙasa domin ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci a Jamhuriyar ta Nijar, ko tayar da zaune-tsaye a ƙasar.
Mohammed Idris ya ce shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban ECOWAS yana gudanar da jagoranci da ya kira ‘abin koyi’.
”Kuma Najeriya na iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da ɗorewar danganta mai tarihi tsakaninta da Jamhuriyar Nijar”, in ji ministan.
Ministan yada labaran Najeriya ya ce dakarun ƙasar, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen da ke yaƙi a Tafkin Chadi, na samun nasara a yaƙin da suke yi da ‘yanta’adda a yankin.
”Don haka, hikima wani ya yi zargin cewa Najeriya za ta haɗa baki da wata ƙasar waje domin wargaza zaman lafiya da tsaron makwabciyarta”, in ji Mohammed Idris.
Dangane da zargin wasu jami’an gwamnatin Najeriya da Janar Tchiani na cewa suna ɗaukar nauyin ‘yanta’adda da ba su horo kuwa, ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce babu ƙamshin gaskiya game da zargin.
”Gwamnatin Najeriya ko wani jami’inta ba su taɓa sanya hannu a bai wa ‘yanta’adda tallafin makamai domin kai wa Nijar hari”, in ji shi.
Haka kuma ministan ya musanta zargin bai wa Faransa wuri domin kafa sansanin.
”Najeriya ba ta taɓa bai wa wata ƙasar waje damar kafa sansanin soji a ƙasarta ba”.
‘Zarge-zarge ne marasa tushe balle makama’
Haka kuma ministan ya musanta zargin da shugaban na Nijar ya yi wa Najeriya na yi wa bututun manta da harkokin noman ƙasar zagon-ƙasa.
Mohammad Idris ya ce Najeriya ta riƙa gudanar da abubuwa na tallafa wa tattalin arzikin Nijar ta hanyar shirye-shiryen samar da makamashi, kamar shimfiɗa bututu iskar gas, na ‘Trans-Saharan Gas Pipeline’, da shimfiɗa layin dogo daga Kano zuwa Maraɗi.
”Babu hikima mutum ya yi tunanin cewa Najeriya na yi abin da zai durƙusar da tattalin arzikin Nijar”.
Kan batun zargin hadin bakin Najeriya da Faransa wajen kafa cibiyar Lakurawa a jihar Sokoto, ministan ya ce zargi ne maras tushe.
”Najeriya ta kasance ja gaba a yaƙi da ta’addanci, inda take sadaukar da kuɗaɗe masu yawa da rayukan jami’anta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi”, in ji Mohammed Idris.
Za mu yi bincike – Majalisar Dattawan Najeriya
Asalin hoton, President of the senate/X
A nata ɓangare, majalisar dattawan ƙasar – wadda yanzu take hutun – ta alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan wadannan zarge-zarge, da zarar ta koma baikin aiki.
Babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Tahir Munguno – wanda ke wakiltar arewacin Borno, ya ce ya kaɗu da waɗannan manyan zarge-zarge da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi kan gwamnatin Najeriya.
Cikin zantawarsa da BBC , Sanata Munguno ya ce bisa tsarin dokokin Najeriya, dole idan za a kawo sansanin sojin wata ƙasa zuwa Najeriya, to dole ne sai an nemi sahalewar majalisar dattawan ƙasar.
”Amma mu daga ɓangarenmu har yanzu, babu wata buƙata mai kama da haka da shugaban ƙasa ya aiko mana majalisa”, in ji shi.
Amma ya ce da zarar majalisar ta ƙare hutunta za ta gudanar da bincike kan wannan batu.
”Za mu gayyaci ministan tsaro da babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, mu ji gaskiyar wannan zargi”, in ji shi.
Mene ne martanin Faransa?
Asalin hoton, AFP
Kawo yanzu, Faransa ba ta ce komai ba ahukumance dangane da waɗannan zarge-zarge duk da cewa a baya ta sha musanta irin wadannan kamalami na shugaban mulkin sojin na Nijar.
Tun a watan Yulin 2023 ne dai Janar Tchiani ya jagoranci kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum tare da korar dakarun Faransa daga Nijar.
Tun daga lokacin, aka riƙa samun zaman tankiya tsakanin Nijar da tsohuwar uwargijiyarta, Faransa, inda har Nijar ta nemi Faransa ta janye dakarunta daga ƙasar.
Buƙatar da Faransa ta amince da ita, inda ta janye dakarunta da ke yaƙi da ‘yan bindiga a fa din ƙasar.