Tsohon firaministan Nijar Hamma Amadou ya rasu yana da shekara 74 da haihuwa.
Kafofin yaɗa labarai na Nijar da Faransa sun ruwaito cewa Hama, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin Nijar ne, ya rasu ne sakamakon jinya a babban asibitin birnin Yamai ranar Laraba da tsakar dare.
Haka nan, tsohon madugun adawa ne kuma jagoran jam’iyyar Modern FA Lumana.
Hama Amadou babban jigo ne a siyasar Nijar, wanda ya riƙe muƙamai da dama. Ya riƙe muƙamin firaminista sau biyu – daga 21 ga watan Fabrairun 1995 zuwa 27 ga Janairun 1996 ƙarkashin shugabancin Mahamane Ousmane.
Sai kuma a karo na biyu daga 31 ga watan Disamban 1999 zuwa 7 ga Yunin 2007 a ƙarƙashin Mamadou Tandja.
A shekarar 2011 ne aka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2013.
Sai dai ya shiga cikin garari a watan Agustan shekarar 2014, inda ya gudu zuwa Faransa bayan an zarge shi da hannu a badakar safarar jarirai daga Najeriya.
Ya koma Nijar a watan Nuwamban 2019 bayan kwashe fiye da shekara biyar yana gudun hijira a Faransa.
Wane ne Hama Amadou?
An haifi Hama Amadou ne a shekarar 1950 a garin Youri na jihar Kollo da ke jihar Tillabery.
Ya yi karatun aikin kwastam da na gwamnati a makarantar koyon aikin gwamnati, ENAM da ke birnin Yamai da kuma babbar cibiyar koyon aikin gwamnati ta kasa da kasa da ke birnin Paris na Faransa.
Hama Amadou ya rike manyan mukamai daban-daban na gwamnati daga 1972 har zuwa 1988, lokacin da ya zama ministan yada labarai.
A lokacin babban taron kasa na Conference National a shekarar 1991, Hama Amadou ya tsaya kai da fata wajen kare jam’iyyar MNSD-Nasara, wadda ya wakilta a wajen taron, abin da ya ba shi damar zama Babban Sakataren jam’iyyar a 1991.
Hama Amadou ya rike mukamin firaministan Nijar har sau uku tsakanin 1995 da 2007, lokacin da majalisar dokokin kasar ta kada kuriar yanke ma shi kauna.
A shekarar 2008 hukumomi sun kulle shi a gidan kurkukun Koutoukale, inda ya shafe wata 10 bisa zargin cin hanci.
Daga bisani ya fice daga jam’iyyar MNSD-Nasara domin kafa jam’iyyarsa ta Modern FA Lumana.
Sau uku kuma ana zabar shi a matsayin dan majalisar dokoki.
A zaben shugaban kasa na 2011 ya zo na uku, kuma ya marawa Mamahadou Issoufou baya a zagaye na biyu.
Hakan ya sa ya samu mukamin shugaban majalisar dokoki har zuwa 2014, lokacin da ya fice daga kasar saboda zargin da ya ke fuskanta na kasancewa da hannu a wata badakala ta sayo jarirai daga Najeriya.
Daga nan, an kama shi yayin da ya koma gida a watan Nuwamban 2015.