- Marubuci, Chiagozie Nwonwu, Fauziyya Tukur, Olaronke Alo, da Maria Korenyuk
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen Yaƙi da Labaran Ƙarya na BBC
Matasa ƴan wasan ƙwallon ƙafa suna saurron taken kasar Rasha kafin a fara wasa. A kusa da su kuma masu zane na zana hoton Shugaban Rasha Vladimir Putin a wani bikin zane da ake gudanarwa.
Maraba da zuwa Burkina Faso, ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da Rasha ke haɓaka ayyukanta domin ƙara samun tasiri.
Binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa Rasha na amfani da kafofin yaɗa labarai da al’adu wurin janyo hankalin ƴanjarida da masu mabiya da yawa a shafukan sada zumunta da dalibai a Afirka yayin da take yaɗa labaran ƙarya.
Wata sabuwar kafar yaɗa labarai na Rasha ne mai suna ‘African Initiative’ ne ke yaɗa wadannan manufofin. Tana iƙirarin cewa ita kafa ce da ke cike giɓin sadarwa da ke akwai tsakanin Rasha da Afirka. Tana amfani ne da kayan aikin da ta gada daga ƙungiyar sojojin haya ta Wagner wanda aka wargaza kuma masana na ganin cewa tana da alaƙa da hukumomin leƙeb asiri na Rasha.
Kafar ta African Initiative an yi mata rajista ne a Watan Satumban 2023, wata guda bayan mutuwar shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin a hatsarin jirgin sama, kuma ta ɗauki tsofoffin ma’aikatan ƙungiyar ta Wagner.
Its efforts have been particularly focused on the three military-run countries of Mali, Niger and Burkina Faso.
Ayyukan African Initiative sun fi mayar da hankali ne kan ƙasashe uku da ke ƙarƙashin mulkin soji da suka haɗa da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.
Bayan juyin mulkin da aka yi a waɗannan ƙasashen, gwamnatocinsu sun yi hannun riga da ƙasashen yammacin duniya da su ke ƙawance da su a baya kamar Faransa, inda suka soki rashin nasarar da ta yi a yƙin da ake yi da ƙngiyoyi masu iƙirarin jihadi. Sun kuma karkata akalarsu ne zuwa Rasha.
Baya ga abubuwan da suka shafi al’adu da take gudanarwa a ƙasa, African Initiative tana da wani shafin labarai na intanet inda ta ke wallafa labarai da harshen Rashanci da Ingilishi da Faransanci da kuma Larabci. tana kuma da tashar bidiyo ta musamman da kuma tashoshi biyar a dandalin Telegram, wanda ɗaya daga cikinsu yana da masu biyan kuɗi kusan 60,000.
Wasu daga cikin tashoshi na Telegram an sake sarrafa su ne daga tsofoffin waɗanda ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Wagner suka kafa. Su ne na farko da suka tallata rundunar tsaron Rasha da ake kira Africa Corps, wanda ta maye gurbin ɓangaren soji na Wagner a yammacin Afirka.
Labaran da ke goyon bayan fadar Kremlin da bayanai masu durmuyarwa, musamman ma game da Amurka na da ɗimbin yawa.
Labarun da ke shafin intanet ɗin Africa Initiative sun yi bayani ba tare da wata ƙwaƙwarrar hujja ba cewa Amurka na amfani da Afirka a matsayin wani fagen gwajin makamai, inda ta ci gaba da yaɗa labarai daga fadar Kremlin da aka daɗe da yin watsi da su.
Labarin dai yan ƙara yayata iƙirarin Kremlin mara tushe ne game da yadda aka tattaro dakunnan gwaje-gwajen makamai daga Ukraine zuwa Afirka. Wani labari mara hujjan kuma ya ci gaba da cewa Amurka na ƙara yawar ɗakunan gwaje-gwajen makamai da ke nahiyar , yana mai cewa “a ƙarƙashin tsarin bincike da ayyukan jin ƙai, nahiyar Afirka ta zama tamkar filin gwaji ga Pentagon”, yana nuna cewa ana gudanar da gwaje-gwajen ilimin halittu a asirce.
Yayin da farfagandar Prigozhin ta fi mayar da hankali kan Faransa, ”Africa Initiative ta fi karkata akalarta ne kan Amurka” in ji mai bincike Jedrzej Czerep, shugaban sashen da ke kula da Gabas ta Tsakiya da Afirka a Cibiyar Harkokin ƙasa da ƙasa ta Poland. “Ta fi adawa da Amurka.”
A watan Yuni, an gayyaci ƙungiyar marubuta a shafukan intanet da kuma ƴanjarida daga ƙasashe takwas don gudanar da abin da aka kira “yawon ƴanjarida” na kwanaki bakwai na yankunan da Rasha ta mamaye a Ukraine.
Kafofin yaɗa labaran Rasha da jami’an ƙasar da ƙasashen Yammacin Turai suka ƙaƙaba wa takunkumai ne suka shirya wannan tafiya, kuma ƴanjaridar sun ziyarci hedikwatar African Initiative da ke birnin Moscow.
”Afirka ba ta samun bayanai game da yakin,” Raymond Agbadi, wani marubucin intanet a Ghana kuma masanin kimiyya da ya yi karatu a Rasha wanda ke cikin tawagar ”yawon ƴanjarida”, ya shaida wa BBC cewa: “Duk bayanan da muka samu ba masu gamsarwa ba ne da za su ba mu damar fahimtar ainihin musabbabin yakin.”
Ba’amurke mai mabiya da yawa a shafukan sada zumunta, Jackson Hinkle, mai goyon bayan shugaban Rasha Vladimir Putin wanda ya daɗe yana yaɗa labaran ƙarya game da Ukraine, shi ma yana cikin tawagar ƴanjaridan.
Bayan sun ziyarci birnin Moscow, ƴanjaridar sun yi tafiya mai nisan kilomita 1,250 zuwa birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa na Ukraine a yankin Donetsk. Daga nan sai suka tafi garuruwan da ke yankin Zaporizhzha – dukkanin yankunan da Rasha ta kwace iko da su a farkon mamayar da ta yi wa Ukraine.
A duk tsawon wannan ziyarar, ƴan jaridan sun samu rakiyar jami’an ƙasar Rasha kuma sun yi tafiya ne da sojojin ƙasar a cikin motocin da ke dauke da alamar Z – wanda alama ce ta mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
A watan Mayu, African Initiative ta shirya wani rangadin manema labarai na daban zuwa garin Mariupol da Rasha ta mamaye da tawagar marubuta a intanet daga Mali.
Ana amfani da waɗannnan rangadi na manema labarai wurin yunƙurin tallata manufofin wata ƙasa. Amma yayin da “Kafofin yaɗa labarai na yammacin Turai ke horar ƴan jarida don bayar da rahoto game da muhimman batutuwan da suka zama damuwa a duniya, Rasha tana amfani da waɗannan tafiye-tafiyen da aka shirya a matsayin hanyar yaɗa labaran da da za su taimaka mata wurin cimma manufofinta ,” in ji Beverly Ochieng, babbar mai nazari Cibiyar kula da dabaru da nazari kan harkokin ƙasa da ƙasa, ta yi nuni da cewa, kasar China ma takan shirya irin waɗannan rangadi.
Samun ƴan jarida na Afirka suna bayar da rahoto game da tafiye-tafiyensu yana nuna kamar da “alamar gaskiya” saboda “suna isar d sakonni ga masu sauraro a harsunan da suke fahimta”, maimakon yin kama da wani ɓangare na “shirin da aka yi na musamman don yi wa Rasha gyaran fuska,” in ji Ms Ochieng.
A cikin labaran da aka wallafa tun bayan tafiyar, ƴan jaridun na Afirka suna kiran garuruwan Ukraine da sojojin Rasha suka mamaye a matsayin “yankin da ake rikici a Rasha” tare da ambaton hukumomin Rasha masu yaɗa farfagandar gwamnatin Rasha tare da gabatar da ra’ayin Kremlin game da iyakokin Ukraine.
A cikin wani labari da aka wallafa a shafinJoyOnline, wani shafin labarai na Ingilishi, ɗan jaridar Ghana Ivy Setordjie ta rubuta cewa yankin Zaporizhzhia na Ukraine (wanda babban birninsa ke ƙarƙashin ikon Ukraine) yanki ne ” a kudancin Rashan Turai.”
Ta shaida wa BBC cewa ba ta amince da cewa Rasha ta mamaye yankunan ba bisa ƙa’ida ba, tana mai tabbatar da cewa rahotannin nata na bayyan na ta ra’ayin ne “amma ba ta karkata zuwa ɓangaren” kasar ba.
Bayan rangadin manema labarai, kafafen yada labarai na cikin gida da ke haɗin gwiwa da Africa Initiative a yankin Sahel na Afirka ta Yamma sun ba da himma a ƙoƙarin wayar da kan al’umma da nufin haɓaka kimar Rasha.
BBC ta bibiyi tashoshi na Telegram na African Initiative da shafukan Facebook, inda ake yada bidiyo, da hotuna, da rahotannin ayyukansu.
A Burkina Faso, mun sami rahotanni game da gasar ƙwallon kafa inda aka buga taken ƙasar Rasha, akwa kuma “darussan abokantaka” a makarantun da ake koyar da dalibai game da Rasha, da tarukan wayar da kai kan ba da agaji na farko ga ƴan ƙasa da ƴan sanda, da kuma bikin zane-zane inda mahalarta suka zana shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin tare da tsohon shugaban Burkina Faso Thomas Sankara, wanda African Initiative ne ta dauki nauyin shiryawa.
Hotuna sun kuma nuna yadda ƴan ƙungiyar Africa Initiative ke rarraba kayan abinci ga mazauna yankin da kuma yadda ake watsa shiri na musamman kan ƙungiyar Wagner mai suna ‘The Tourist’, game da wasu ƴan Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda Wagner da ƙawayenta ke taimakawa gwamnati wajen yakar ƴan tawaye.
“Asali ita Africa Initiative shiri ne da zai shafe duk wani abu da Prigozhin ya yi kuma a maye gurbinsa da wani sabon shiri. Daga baya a cikin wannan tsari, ya bayyana cewa ya fi dacewa a sake amfani da duk kadarorin da ke can,” in ji mai bincike Mista Czerep daga Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa ta Poland.
Hukumar Tsaro ta Tarayyar Rasha, FSB, tana taka muhimmiyar rawa a cikin sabuwar ƙungiyar, in ji shi. Shugaban kuma babban edita na Africa Initiative shine Artyom Kureyev, wanda masana harkokin Rasha suka bayyana a matsayin jami’in Hukumar Tsaron Tarayyar Rasha. Mista Kureyev yana da alaƙa da Valdai Club, cibiyar samar da dabaru da ke Moscow wanda ke da kusanci da Shugaba Putin.
Shafin intanet na African Initiative ya bayyana Anna Zamaraeva, tsohuwar jami’ar yaɗa labarai ta Wagner, a matsayin mataimakiyar babban editanta.
Viktor Lukovenko, wanda aka sani a matsayin ɗaya daga cikin “masu fasahar siyasa” na Prigozhin, ya kafa ofishin Burkina Faso na Afirka Initiative amma ya bar mukamin a cikin ƴan watannin baya bayan nan. Wani tsohon mai kishin ƙasar Rasha wanda baya aka alaƙanta da aikata laifuka, Mista Lukovenko ya shafe shekaru biyar a gidan yari saboda harin da aka kai a Moscow kan wani ɗan ƙasar Switzerland wanda daga baya ya mutu.
Mun tuntubi African Initiative don yin sharhi. Ofishinta da ke Moscow ya tabbatar da cewa sun karɓi tambayoyinmu amma ba mu sami wata amsa ba. Mun kuma tuntubi gwamnatin Rasha amma su ma ba mu sami amsa daga wurinsu ba.
A cikin watan Fabrairu, a wani martani da aka mayar kan rahoton da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, wata ƙasida a shafin intanet na African Initiative ta bayyana cewa hukumar editocinta “ta nace cewa manufarta ita ce yaɗa ilimi game da Afirka a Rasha da kuma ɗaukaka martabar Rasha a ƙasashen Afirka”, inda ta bai wa ” ‘Yan Afirka damar faɗa kum a sauraresu, musamman game da sukar da suke yi wa ƙasashen Yamma”.
A halin yanzu, ƙungiyar na ci gaba da ƙara ƙaimi wurin yaɗa manufofi a yankin Sahel. A makon ƙarshe cikin watan Agusta, dalibai kusan 100 a Burkina Faso sun halarci wata tattaunawa kan damar samun horo a kasar Rasha.
“Na koyi abubuwa da dama kan al’adun Rasha da kuma dangantakar dake tsakanin gwamnatocinmu,” in ji wani matashi da ke sanye da riga mai ɗauke da tambarin African Initiative a wani bidiyo da aka naɗa bayan tattaunawar.