Minista Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin an kawo sauyi a fanin samar da wutar lantarki da zai haifar da habbaka tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Da yake tsokaci kan batun, kwararre a fanin Tattalin Arziki Shu’aibu Idris Mikati ya ce ‘yan siyasa sun jawo wa kasar asara da dama a wannan fanin, inda ya ce samun wutar lantarki ya kasu kashi kashi, saboda haka dole ne Minista Adebayo ya fayyace wa al’umma abinda ya ke nufi da cewa dalar Amurka biliyan 10 zai iya ba wa ‘yan kasa wuta har na sa’o’i 24 a rana. Mikati ya ce an kwashi shekaru da dama kan kokarin samar da wutar lantarki, kuma an kashe dalar Amurka fiye da biliyan 40 ko 50, amma ba a shawo kan matsalar ba.
A nashi bayanin, masanin tattalin arziki na kasa da kasa Yusha’u Aliyu ya ce dole ne a duba bunkasar yawan al’umma da cigaban su kafin a fara batun samar da wutar lantarki musamman ma a shiyar Arewa.
Yusha’u ya ce wadannan kudade dalar Amurka biliyan 10, idan an same su za su zama suna da muhimmanci ga tattalin arzikin kasar amma sai an tsaya da gaske, saboda abu ne da za a yi ta yi akai akai domin a baya ma an kashe dalar Amurka biliyan 16 ko fiye, amma ba a samu wadatuwar wutar ba. Yusha’u ya ce matsalar rashin wutar ta fi yawa a Arewa, inda ya bada misali da wasu jihohi da ke gabashin kasar irin su Jihar Abia da ya zuwa yanzu ta yi shekaru 3 tana samun wadatacciyar wuta ta wata hanya daban. Yasha’u ya ce duk kudin nan da aka kashe a baya, megawat dubu 5 ne kadai ake da shi a kasar, kuma komin yawan kudi, karfin watan bai taba wuce haka ba.
A nata bayanin, Hajiya Fatima Abubakar ta ce sauya halayen ‘yan Najeriya ne zai kawo canji da zai kai ga samun wutar lantarki ingantacciya ta hanyar gaskiya.
Saurari cikakken rahoton: