A ranar Juma’a aka bukaci gwamnatin Birtaniya da ta dago batun babban dakaren kafar yada labaran nan mai rajin democradiyya da aka daure, Jimmy Lai, ga China, bayan da rahotanni suka bulla cewa, ministan harkokin waje David Lammy na shirin zuwa Beijing.

Lai, mai shekaru 76, ne mamallakin shahararriyar mujuallar nan ta Apple Daily da ta rika goya bayan dandazon masu zanga-zangar tabbatar da Democradiyya a matattarar mai cike da harkokin tattalin arziki.

Ana tsare da shi ne tun a shekarar 2020, inda yake jiran ayi mishi shari’a bisa tuhumar da ta hada da hada baki da dakarun kasashen ketare da tunzura jama’a su yiwa gwamnati bore.

Rukunin lauyoyin shi a Landan sun bayyana fatan su na ganin Lammy yasa batun Lai a gaba gaba, a yayin ziyarar ta shi, wadda ba’a riga an tabbatar da ita ba.

Lauya Caoilfhionn Gallagher ya shaidawa manema labarai cewa, an bayyanama gwamnatin Ingila karara cewa, indai har tana nema saisaita hulda ne tsakanin ta da China, to kuwa akwai bukatar yin amfani da wannan damar wajen tabbatar da ganin an saki Jimmy Lai.

A yayin wani biki na kungiyar manema labarai masasa shinge a Landan. Dan Jimmy Lai, Sebastien yace mahaifin shi, wanda ke da takardar zama dan kasar Birtaniya, na cikin mawuyacin hali na tabarbarewar lafiyar sa, sakamaon kasancewa a tsare cikin kadaici na kusan shekaru 4.

Ya kara da cewa, lafiyar shin a iya kara tabarbarewa a ko yaushe.

An fara tafiyar hawainiya a shari’ar ta Lai ne a watan Disambar shekarar 2023, inda ake sa ran ya bada shaida a karon farko a ran 20 ga watan Nuwamba.

Sebastien yace, a yanzu sama da ko yaushe, gwamnatin Birtaniya keda bukatar tsayuwar daka a bayan mahaifin shi, da daukar lamarin da muhimmanci, sama da yadda tayi a baya,

Da Sebastien din da tawagar lauyoyin Jimmy Lai sun gana da jami’an ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya, to amma Gallagher yace, ko kadan basu ji dadin ganin yadda, daga Lammy har priminstan na Birtaniya Keir Starmer ba wanda ya gana da dan na Jimmy Lai.

Gallagher yace, inda da batun nada muhimmanci ga gwamnatin Birtaniya, me ya hana ace sakataren harkokin wajen kasar ganawa da Sebastien, ko ganawa kai tsaye da priministan kasar.

By Ibrahim