Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula Da Silva, zai yi amfani da damarsa ta mai masaukin baki ya tallata batutuwan dake ransa, da suka kunshi yaki da yunwa da fatara da sauyin yanayi da tatsar haraji daga hannun manyan attajirai.

Sai dai ana ganin yake-yaken da suka yi matukar raba kawunan mambobin kungiyar ta G-20 suma zasu mamaye tattaunawar da za’a yi a taron.

Shugaba Biden na Amurka zai halarci a karo na karshe, sai dai halartar Xi Jinping na China da ake yiwa kallon shugaba mafi tasiri a taron na bana zai dusashe nasa hasken.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai halarci taron a bisa gayyatar takwaransa na Brazil kuma shugaban kungiyar G-20 mai ci, Luiz Inacio Lula da Silva.

Taron wanda zai gudana tsakanin Litinin 18 da Talata 19 ga watan Nuwanbar da muke ciki, zai tattaro shugabanni daga kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya, ciki har da tarayyar Turai da takwararta ta nahiyar Afrika da hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa.

Najeriya ta jima tana neman ayi garanbawul ga tsarin hukumomin dake jagorancin duniya kuma sau da dama tana gabatar da cancantarta a matsayin mai takarar kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Ana sa ran Shugaba Tinubu ya gudanar da tarurrukan kasa da kasa a gefen taron na G-20 da nufin bunkasa sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya.

By Ibrahim