Muhinman batutuwa aka tattauna tsakanin tawagar manyan jami’an gwamnatin na kasar Jamus karkashin jagorancin jakadan kasar a Nijar Dr. Schnakenberg Olivier da kuma mahukuntan jihar Agadas a yayin wata ziyarar kwana biyu da suka kai Agadas.
Jami’an na tawagar Jamus sun yiwa hukumomin jiha karin haske game da irin tallafin da suke baiwa jihar, dama kasar Nijar domin bunkasa tattalin arziki da kuma ababen more rayuwa da kuma baiwa hukumomin na Nijar kwarin gwiwar aiki tare domin shawo kan matsalolin da suka yi yawa a kasar.
Ekbene Cornac dake cikin tawagar ya ce makasudin wannan ziyarar shine su fahimci tarin matsalolin da jihar ke fuskanta domin yin aiki tare da hukumomin wajen shawo kan su.
Ya ce “kun san ayyuka da dama ne tarayyar Jamus ta yi a cikin jihar Agadas da ma sauran sassan kasar, kuma jihar na da matukar muhimmanci ga kasashen mu na Turai musanman wajen tabbatar da tsaro”.
Hukumomi a jihar Agadas na fatan ganin a wannan karo huldar za ta anfani kowane bangare na al’umma inji Oumarou Ibrahim Oumarou mai martaba sarkin Abzin.
Wannan ziyarar na zuwane a dai dai lokacin da aka shiga takun saka tsakanin gwamnatin mulkin sojin kasar Nijar da kuma kungiyar tarayyar Turai kan wani tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, saboda haka masu fashin baki irin su AbdulAziz Ibrahim ke ganin ya kamata gwamnatin Nijar ta yi taka tsan-tsan da kasashen Yamma.
Anasu bangare kungiyoyin dake sa ido kan rayuwar al’umma na fatan wannan karon tallafin da kasar Jamus za ta baiwa kasar yazo hannuwan wadanda aka yi dominsu.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud: