Tsayuwar Arafa ɗaya ce daga cikin rukunnan aikin Hajji, ɗaya daga cikin ibadar Musulmi mafiya girma.
Filin Arafat na da nisan kimanin kilomita 24 daga garin Makkah, kuma a nan ne mahajjata za su shafe wunin yau Alhamis.
Sheikh Ibrahim Mansur malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, kuma ya ce akwai maganganun malamai uku dangane da asalin sunan ranar Arafa.
Magana ta farko, an kira ta Arafa ne saboda a lokacin ne mutane daga sassa daban-daban ke sanin juna saboda haɗuwa a wuri guda. Sai ake kiranta Arfa, kamar yadda malamin ya yi bayani.
Na biyu kuma, wasu malamai sun ce mala’ika Jibrilu ya ɗauki Annabi Ibrahim yana kewayawa da shi don nuna masa alamomi na aikin Hajji.
To idan ya nuna abu sai ya tambaye shi, “Aarafta, Aarafta” da Larabci – wato ka gane?. Shi kuma Annabi Ibrahim sai ya ce “Araftu, Araftu” – na gane, na gane.
”Wannan dalilin ne ya sa aka saka mata Arafa”, in ji malamin.
Magana ta uku, lokacin da Allah ya sauko da Annabi Adam da Nana Hawwa’u zuwa duniya sun daɗe ba su haɗu ba. Amma da Allah Ya tashi haɗa su sai ya haɗa su a ranar Arafa.
”Wannan haɗuwa da suka yi suka gane juna, sai ya sa ake kiran ta Ranar Arafa”, kamar yadda ya yi bayani.