Masu sana’ar sayar da dabbobi a Nijar na ci gaba da kokawa da yanayin da suka tsinci kansu, bayan matsalolin da matakin gwamnatin ƙasar na hana fita da dabbobi ƙasashen waje ya haifar.

A kasuwannin dabbobin da ke birnin Yamai, raguna na nan maƙare babu ma su saya, wanda ya janyo asara mai dumbin yawa ga masu sayar.

Wasu ma su sayar da ragunan da BBC ta tattauna da su a Yamai sun ce wasu ragunan har mutuwa suke yi saboda rashin saye.

Malam Inusa, mai kawo dabbobi kasuwar Yamai daga Tasawa, ya shaida wa BBC cewa a yanzu dabbobi na nan birjik babu ma su saya.

Ya ce, “Ga ragunan nan har babu ma inda za a ajiye su saboda yawansu amma babu masu siya; tun yanzu, a wuni guda da ƙyar za ka sayar da rago guda.”

Alhaji Lawwali Kalla, mazaunin Yamai, ya shaida wa BBC cewa rashin siya raguna na da nasaba da albashin ma’aikata da ba a biya ba.

Ya ce, “Da yawan ma’aikata sun ce ba a biya su albashi ba, shi ya sa ba su je sun sayi ragunan layyar ba.”

Kwantan raguna a Jamhuriyar Nijar na zuwa ne a yayin shirin gudanar da sallar layya ta shekarar 2025 ga ma su iko.

A watannin baya, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da haramcin fitar da dabbobi daga ƙasar zuwa ƙasashen waje, ciki har da Najeriya.

Alƙaluman cinikayyar ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa a shekarar 2023, Nijar ta fitar da dabbobin da suka kai na dala miliyan 3.93 zuwa Najeriya.

Ministan kasuwancin ƙasar ya ce gwamnati ta umarci jami’an tsaro su dau matakan da suka dace a kai da kuma hukunta duk wanda ya saɓa wa sabuwar dokar.

By Ibrahim