Asalin hoton, efcc
Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin ɗaurin wata shida ga Abdullahi Musa Hussaini, wanda aka fi sani da “Amuscap”, bisa laifin liƙi da naira a lokacin bikin aurensa a watan Disamba.
Hukuncin ya biyo bayan amsar laifin da aka tuhumarsa.
Ana liƙi ko watsa takardar kuɗi a Najeriya, musamman lokacin bukukuwa da suka shafi aure, domin nuna farin ciki.
Duk da haka, hukumar EFCC ta yi gargadi kan yiwuwar liƙi da kuɗi a irin wannan lokaci, tana mai cewa hakan na nuna rashin mutunta kuɗin naira.
Amuscap yana daga cikin ‘yan Najeriya da aka hukunta bisa saɓan dokar babban bankin Najeriya (CBN) ta 2007.
Dokar ta ce liƙi da rawa da kuɗin naira laifi ne, hukuncin sa shine ɗaurin wata shida a gidan yari ko cin tarar 50,000.
EFCC ta yi zargin cewa Amuscap ya liƙa tare da taka kuɗi naira 100,000 a lokacin biki.
A shekarar da ta gabata, shahararren ɗan daudun Idris Okineye, ko Bobrisky, da jarumar Nollywood Oluwadarasimi Omoseyin sun sha hukuncin ɗaurin wata shida saboda wannan laifi.