Asalin hoton, Assimi Goita
Bayanan hoto,
Shugaban ƙasar Mali, Assimi Goita
Hukumar Ƙungiyar cigaban ƙasashen yammacin Afirka, Ecowas, ta nuna damuwa kan rashin jituwar da ta ɓalle tsakanin ƙasar Mali da maƙwafciyarta Algeria, lamarin da ya kai ga ƙasashen biyu janye jakadunsu daga juna.
A cikin wata sanarwa da ta fitar yau a Abuja, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin ƙasar Mali da kuma Algeria, kamar yadda za a iya gani a jerin sanarwar da dukkanin ɓangarorin biyu suka fitar.
A madadin ƙasashen da ke da wakilci a cikinta, Ecowas na nuna matuƙar damuwarta kan lamarin. Tana kuma kira ga Mali da Algeria da su yayyafa wa wutar lamarin ruwa, su buɗe hanyoyin tattaunawa sannan su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya na yanki da nahiya wajen warware saɓanin ra’ayin da ke tsakaninsu.
A makon da ya gabata ne Algeria ta kaɓo wani jirgi maras matuƙi mallakin sojojin ƙasar Mali, wanda ta ce ya karya dokokin kan iyakar ƙasarta.
Mali ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadanta da ke Algeria kiranye, haka nan ma ƙasashen ƙungiyar yankin Sahel na AES, sun bi sahun Mali ta hanyar ɗaukar irin wannan mataki.
Lamarin da ya sanya ita ma Algeria ta yi wa jakadunta da ke Mali da Jamhuriyar Nijar kiranye, sannan ta ce za ta jinkirta tura jakadanta zuwa Burkina Faso, wadda ita ma mamba ce a ƙungiyar ta AES.
Hakan nan ƙasar ta Algeria ta fitar da sanarwa ɗauke da kausasan kalamai, sannan ta yi fatali da zargin da Mali ke mata kan cewa tana ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.