Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Social Media

Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sauya sheƙa da ƙulla ƙawance tsakanin ƴan siyasa na daga cikin manyan ginshiƙan tsarin dimokraɗiyya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar PDP ya ce ƴan siyasa na iya yin waɗannan ƙa’idodin, domin an yi hakan a baya, kuma an yi ainun za a yi a nan gaba.

Kalaman Atiku na zuwa ne yayin da ake ta raɗe-raɗen cewa jam’iyyun hamayyar ƙasar za su haɗu domin tunkarar APC mai mulki a zaɓen 2027.

A cikin makon nan, Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, tare da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, wanda ya taya Atiku takara a matsayin mataimaki a zaɓen 2023, sun fice daga PDP, inda gwamnan ya bayyana komawarsa jam’iyyar APC, mai mulkin ƙasar.

Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda hakan ya haifar da muhawara a cikin al’umma.

Atiku ya kare wannan matakin, yana mai cewa ya ziyarci Buharin a matsayin dattijo a fagen siyasar Najeriya.

”A 2013 an yi ƙawancen haɗakar ƴan adawa, kuma ko a lokacin an nemi shawarwarin tsoffin shugabannin ƙasar nan irin su Obasanjo da Babangida”, inji Atiku.

Atiku ya kara da cewa zaɓen 2027 ba wai yaƙi ne tsakanin PDP da APC ko LP da APC ba, yaƙi ne tsakanin ƴan Najeriya da gwamnati wanda ta sa su cikin uƙuba.

By Ibrahim