- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Abuja
- Twitter,
- Aiko rahoto daga Abuja
Harshen Hausa na ɗaya daga cikin manyan harsunan duniya da suka fi samun karɓuwa a shafukan sada zumunta da kafafen yaɗa labarai a wannan zamani.
Kafin zuwan shafukan sada zumunta na zamani, galibi an fi magana da mafani da harshen Hausa a yankunan jihohin arewacin Najeriya da wasu sassan kudancin Jamhuriyar Nijar da Ghana da wasu ƙasashen Afirka, galibi Afirka Yamma.
To sai dai bayan bayyanar shafukan sada zumunta harshen Hausa ya samu bunƙasar da ba kowane harshe ne ya samu ba a duniya.
Shafukan zumunta sun ɗaukaka harshen Hausa, ta yadda har wasu daga cikin su irin su Facebook suna sanya harhsen cikin harsunan da shafin ke amfani da su.
Masu amfani da harshen Hausa a shafukan sada zumunta a kullum ƙaruwa suke yi, lamarin da masana ke kallo a matsayin wani mizani na auna bunƙasar harshen.
Shafukan sun kuma taimaka wa masu amfani da harshen wajen isar da saƙon su cikin sauƙi da sauri, kamar yadda ‘yancin faɗin albarkacin baki ya ba su damar hakan.
A gefe guda kuma, Hausa harshe ne mai shimfiɗaɗɗun ƙa’idon amfani da shi wajen furuci da kuma rubutu.
To sai dai Masana harshen na cewa duk da bunƙasar da harshen ya samu ta ɓangaren shafukan sada zumunta, a ɓangare guda kuma harshen na fuskantar cikas ko tarnaƙi, ta yadda ake yi masa karan-tsaye wajen amfani da ƙa’idarsa a shafukan na sada zumunta.
Dakta Muhammad Sulaiman Abdullahi mataimakin daraktan cibiyar nazarin harsunan Najeriya da fasahohin al’umma da fassara ta jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce akwai takaici yadda za ka ga mutum ke amfani da harshen Hausa a shafukan sada zumunta a matsayin sana’a, don rufa wa kansa asiri, amma bai mayar da hankali ba wajen koyon amfani da ƙa’idojinn da harshen ya shimfiɗa ba.
Masanin harshen ya kuma zayyano wasu ƙalubale da ya ce shafukan sada zumuntar na haifar wa harshen na Hausa a wannan zamani.
Gajarta rubutu
Wani abu da ke jefa ƙaidar rubutun Hausa cikin barazana shi ne ƙoƙarin da masu amfani da harshen a shafukan sada zumunta ke yi na rage kalmomin domin sauƙaƙa wa kansu aika saƙo.
Dakta Muhammad Sulaiman Abdullahi ya ce kodayake saƙon da masu amfani da harshen ke son isarwa ta hanyar taƙaita kalmomin na isa, amma hakan ya saɓa ƙa’ida yadda aka amince a rubuta harshen.
”Kodayake masana harshen na ɗaukar wanan sabon salo na gajerta rubutu a matsayin ci gaba da bunƙasar harshen, amma hakan na yi wa ƙa’idojin rubutun Hausa tarnaƙi a wasu lokuta, saboda ba a ko’ina ne aka amince da gajartawar ba”, in ji shi.
Galibi abin da ke janyo amfani da salon gajartwar shi ne wasu shafukan sada zumuntar kan kayyade adadin kalmomin da za a yi amfani da su a wani dandali, kamar shafin X da a baya aka fi sani da Twitter, za ka tarar da cewa an iyakancewa mutum adadin haruffan da zai yi amfani da su, don haka ta sa tilas aka ɓullo da salon gajartawa domin samun damar isar da saƙon, kamar yadda Dakta Muhammad ya yi ƙarin haske.
Akwai kalmomin da suka yi fice wajen gajartwa a shafukan sada zumunta da suka haɗa da:
Malamin jami’ar ya ce ci gaba da amfani da irin wanan salo ko shakka babu zai iya kawo cikas ko tarnaƙi ga ka’idojin rubutun Hausa.
Ya ci gaba da cewa kasancewa kalmomi ne kawai ake taƙaitawa, to hakan zai sa a yi amfani da haruffa iri ɗaya wajen taƙaita kalmomi mabambanta, wanda kuma hakan zai kawo ruɗani wajen fahimtar ma’anar abin da ake son rubutawa.
”Kuma sannu a hankali masu tasowa da ke amfani da shafukan, waɗanda kuma ba su da ilimin harshen sai su ɗauka hakan daidai ne, to ka ga idan hakan ya ci gaba lallai ƙa’idar rubutun Hausa za ta fukanci cikas”, in ji shi.
Haɗawa da raba kalma
Wannan shi ne babban ginshiƙi a ƙa’idar rubutun Hausa, kuma shi ne fagen da aka fi samun kura-kurai a shafukan sada zumunta.
”Dokar haɗa kalma da raba ta wajibi ne , kuma tilas ne a harshen Hausa, domin kuwa karya wannan ƙa’ida ka iya haifar da mummunar illa ga ma’anar abin da ake son rubutawa”, in ji Dakta Muhammad Sulaiman Abdullahi.
Rabawa ko haɗa kalma kan sauya ma’anar saƙon da ake son isarwa a lokuta da dama, kuma saɓa wannan ƙa’ida abu ne da ke neman zama ruwan dare a shafukan sada zumunta.
(Musa ya ga rigarka) Idan aka haɗe kalmomin ‘ya’ da ‘ga’, sai ya bayar da ma’anar ‘Musa yaga rigarka’, Ma’ana kamar kana bai wa Musa umarnin cewa ya yaga rigarsa, wanda ma’anar ta sha bamban da abin da ake son rubutawa.
(Ya ji daɗi) Idan aka haɗe kalomomin ‘ya’ da ‘ji’, sai ya bayar da ma’anar ‘Yaji daɗi’, wanda ke nufin wata ma’anar daban.
Kalmomin da aka fi haɗe su a shafukan sada zumunta, galibi kalmomi ne masu gaɓa ɗaiɗai.
Haruffa masu ƙugiya
Wata matsala da shafukan sada zumunta ke haifarwa ita ce rashin amfani da haruffa masu lanƙawasa.
Galibi wayoyi da na’urorin da ake amfani da su wajen yin rubutu a shafuka sada zumuntar ba su da haruffa masu lanƙwasa, sai ‘yan ƙalilan.
Dakta Muhamman Sulaiman Abdullahi ya ce dokar lanƙwasa da ta haɗe kalma ko raba ta kamar Danjuma ne da Danjumai ta fuskar sauya ma’anar kalma idan ba a yi amfani da su ba.
”Za ka ga mutum ya zo yana gadara da tinƙaho da harshen Hausa, amma ba ya kulawa da amfani da waɗannan haruffa a shafukan sada zumunta”. in ji masanin harshen Hausan.
Ya bayar da misalai kamar haka:
”Musa ya ɗaiɗaita maƙiyinsa” Idan ba a yi amfani da lanƙwasa kan kalmar ‘ɗaiɗaitawa’ ba ma’amar abin da ake son rubuta wa za ta sauya ta yadda za ta ci karo da abin da ake son rubuta wa, ke nan zai koma ”Musa ya daidaita maƙiyinsa’.
‘Na taka ƙashi’ Idan ba a yi amfani da lanƙwasa ba kan harafin ‘ƙ’ da ke cikin jimlar, to nan ma ma’anar jimlar zai koma ‘Na taka kashi’, wanda kuma ba ma’anarsu ɗaya ba.
Amfani da haruffan da ba na Hausa ba
Haka kuma akwai wasu masu amfani da shafukan zada zumuntar da ake amfani da wasu haruffan da babu su a Hausa wajen ƙoƙarin isar da saƙo cikin rubutu a shafukan.
Misali: Galibi akwai masu amfani da harafin X maimakon harafin Z, wanda galibi hakan ya ci gaba to la shakka masu tasowa za su fuskanci cikas wajen ƙoƙarin fahimtar asalain harafin da ya kamata a yi amfani da shi.
Na xo makaranta – Na zo makaranta.
Xuwa kasuwa – Zuwa kasuwa
Xan shiga mota – Zan shiga mota.
Rashin amfani da alamomin rubutu
Wani abu da masu amfani da shafukan sada zumunta ba su fiya la’akari da shi ba dangane da amfani da harshen Hausa a shafukan sada zumunta shi ne amfani da alamomin rubutu.
Alamomin rubutu, wasu abubuwa ne da ke gyara rubutu tare da tsaftace shi, da kuma fito da cikakkiyar ma’anar sakon da ake son isarwa.
To sai dai galibi masu amfani da harshen a shafukan sada zumunta, kan riƙa rubutu kara zube, ba tare da amfani da alamomin rubutu ba, wanda kuma yin hakan babban kuskure ne, domin kuwa zai sa rubutun ya gimshi masu karatu.
A wasu lokuta masu rubutu kan yi amfani da alamar aya (.) kawai a cikin rubutunsu, wadda ake sakawa a ƙarshen jimla, ba tare da la’akari, da sauran alamomin ba.
Ga wasu alamomin da ba a la’akari da su a shafukan sada zumunta:
Alamar motsin rai (!) – Wannan alama ce da ake amfani da ita domin nuna wani abu da ya ɗarsu ko ya sosa zuciya na farin ciki ko akasin haka. Amma a wasu lokuta sai ka ga ana amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba.
Misali, (sanarwa! sanarwa!! sanarwa!!!)
Wannan kuskure ne, domin kuwa kalmar sanarwa ba ta nuna wani abu da ya sosa zuciya. Sannan masana na cewa kuskure ne sanya alamar fiye da guda a wuri guda (!!); gda ɗaya kawai ake sakawa.
Alamar waƙafi mai ruwa (;) da ake sanyawa tsakanin jimloli biyu kishiyoyin juna. Misali: Ko su zo; ko kar su zo sai yi taronmu.
Ko ta dafa abinci; ko ta ƙi dafawa babu abin da ya shafe ni.
Da sauran alamomin rubutu irin su: baka biyu () da ruwa biyu (:) da karan ɗori (-) da sauransu.
Mafita
Dakta Muhamman Sulaiman Abdullahi ya ce abin da ya kamata a yi don rage ko yaƙi da barazanar da harshen Hausa ke fuskanta a shafukan sada zumunta a wanna zamani shi ne dole ne masu amfani da shafukan su koyi ƙa’idojin harshen tare da amfani da su.
Ya ƙara da cewa duk da cewa matsalar gajarta kalmomi ka iya zama wani sabon salo a isar da saƙon cikin rubutu da harshen, amma yana da kyau a san inda kawai ya kamata a yi amfani da su.
”Ba laifi ba ne mutum ya koyi wannan salo kasancewar yana taimakawa wajen isar da saƙo cikin taƙaitattun haruffa, amma kuma yana da kyau mutum ya san mene ne asali, ta yadda kuma zai yi amfani da shi a wurin da ba a iyakance masa haruffa ba”, in ji shi.
Sannan kuma ya ce yana da kyau manyan kafofin yaɗa labarai na duniya su inganta ƙa’idojin rubutunsu a shafukansu.
Haka kuma ya shawarci masu amfani da shafukan su koma amfani da litattafan da aka rubuta kan ƙa’idojin rubutu, su karanta su, sannan su yi amfani da su a kodayaushe.
”Sannan kuma su riƙa lura da manyan shafukan kafofin yada labarai na duniya da ke amfani da harshen Hausan, hakan ma zai ƙara inganta amfani da ƙa’idojin”, in ji masanin.