Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta bayar da rahoto cewa ƙasar ta kai hari kan cibiyar tattara bayanan sirri ta Isra’ila, wato Mossad.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, Tasnim, ya wallafa jerin hotuna da ke nuna yadda shalkwatar cibiyar Mossad ke ci da wuta.
Tasnim ya ambato rundunar juyin juya halin Iran, inda ta ce an kai wannan hari ne ta amfani da makamai masu linzami.
A cikin wani saƙo da kamfanin dillancin labaran na Iran ya wallafa a shafinsa na Telegram, an bayyana cewa: “Makaman IRGC masu linzami sun kai hari ga cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila, duk da ƙarfin tsaron sararin samaniya na zamani da ƙasar ke da shi.”
Kawo yanzu, Isra’ila ba ta fitar da wani bayani kan wannan iƙirari ba. Saboda dokokin taƙaita yaɗa labarai da gwamnati ta sanya, kafofin yaɗa labarai a ƙasar ba za su iya bayar da labari kan wasu wuraren da aka kai wa hari ba.