Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya sanya hannu kan wata doka mai cike da cece-kuce da ta bukaci dukkan direbobi su biya wasu kudade a matsayin lasisin rediyon motocinsu.
Wannan doka dai ta zo ne a daidai lokacin da wasu da dama ke kokawa kan matsalar tsadar rayuwa a kasar.
Masu sukar lamarin na korafin cewa bai kamata su dauki alhakin tallafawa gidan rediyon gwamnati ba wanda su ke yi wa ganin kafa ce ta tallata jam’iyya mai mulki.
Matakin dai wani shiri ne na fadada hanyoyin samun kudaden shiga ga kafar yada labarai mallakar gwamnatin kasar amma masu sukar lamarin sun ce kudin lasisin ya yi yawa, musamman ganin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
A Zimbabwe ba za ka iya yin inshorar mota ba sai idan ka biya kusan dalar Amurka casa’in a shekara a matsayin kudin lasisin rediyo wanda zai shige aljihun gidan rediyon gwamnati.
Akwai rahotannin mutane na tunanin cire rediyon motocinsu amma ko sun yi hakan ba za su tsira ba domin biyan kudin tilas ne ga duk wani wanda ya mallaki mota a kasar ko da kuwa ba ya sauraron gidan rediyon gwamnati.
Kalubalen da ke gaban gwamnati shi ne bullo da hanyoyin da za ta kara haraji yayin da mutane da yawa ke gudanar da al’amuransu a bangaren yan kasuwan da ba su cikin tsarin biyan haraji a hukumance.
Da yake mayar da martani game da damuwar masu ababen hawa a shafukan sada zumunta, babban jami’i a ma’aikatar yada labarai ta kasar Zimbabwe, Nick Mangwana, ya ce sabuwar dokar ta zama dole kuma an bullo da ita ne saboda tabbatar da daidaito a al’umma.