Hukumar Kwastam ta Najeriya

Asalin hoton, Nigeria custom service/Facebook

Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen yankin Seme, ta kama wata mota da ake zargin tana ɗauke da kayan haɗa bam (IED).

Wannan na cikin bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, inda jami’anta ke binciken motar da aka kama a kan titin Lagos zuwa Badagry.

An gano cewa cikin motar akwai kwanso guda shida na ma’adani mai launin azurfa tare da guba mai ƙarfi da aka fi sani da corrosive mercury, wanda ake kyautata zaton ana amfani da shi wajen haɗa abubuwan fashewa.

Shugaban Kwastam na yankin, Kwanturola Ben Oramalugu, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargin yana da alaƙa da motar.

Ya bayyana cewa nasarar kama motar na nuna yadda Kwastam ke cikin shiri da kulawa wajen kare tsaron kasa.

Oramalugu ya kara da cewa wannan aiki na cikin matakan da Kwastam ke dauka don dakile ayyukan fasa-kwauri da sauran laifuka a iyakokin Najeriya.

Baya ga motar da aka zargina, hukumar ta kuma kama wasu kayayyaki da dama da suka saɓa wa doka.

Kayayyakin sun hada da kuɗaɗen ƙasashen waje daga Birtaniya, Kanada da Amurka da darajarsu ta kai kusan naira miliyan tara, wanda hakan ya saɓa dokar harajin kaya na waje.

Sauran kayayyakin da aka kama sun hada da robar ganyen wiwi guda 553, buhunan shinkafar waje 1,415, jarkokin man fetur guda 750, da kuma magungunan da ba a yi rijistarsu ba.

Kwanturola Oramalugu ya ce hukumar za ta miƙa kayayyakin da aka kama ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike tare da ɗaukar mataki, da gurfanar da wadanda ake zargi.

By Ibrahim