Asalin hoton, Getty Images

Gidan talbijin na ƙasar Iran, Nour News ya bayar da rahoton cewa akalla mutum 78 ne suka mutu, yayin da 329 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra’ila a yayin da aka gudanar da hare-hare a wasu sassa na birnin Tehran da daddare.

Sai dai, kafar a shafinta na Telegram ta ce alƙaluman ba na hukuma ba ne.

“Ba mu tantance waɗannan alƙaluma ba. Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.”

Rundunar sojin Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Iran, inda ta bayyana cewa ta harba babbar cibiyar aikin inganta sinadarin Uranium na Iran a Natanz da kuma lalata filin jirgin sama na Tabriz.

Wakilin BBC ya ce manyan hare-haren na Isra’ila suna da manufofi uku – lalata shirin nukiliya na Iran, kassara ƙarfin kariya da kashe masana kimiyya.

Tun da farko, Isra’ila ta hallaka shugabannin sojojin Iran da dama, ya kuma hallaka shugaban rundunar sojin kasar da babban jagoran sojojin juyin-juya-hali.

Hare-haren Isra’ila sun shafi akalla birane shida, ciki har da yankunan da jama’a ke zaune a babban birnin ƙasar Tehran.

Iran ta mayar da martani da harba sama da jirage marassa matuka dari guda a kan Isra’ila.

Isra’ila ta rufe ofisosin jakadancinta na dan wani lokaci a kasashen duniya, ta bayyana cewa ta kai harin ne domin tabbatar da wanzuwarta.

By Ibrahim