Nijar

Asalin hoton,
Getty Images

A Jamhuriyar Nijar, ƙungiyar harkokin addinin Musulunci ta ƙasar (AIN), ta danganta yawan mace-macen aure da ƙasar ke fama da shi da wasu manyan abubuwa guda uku da suka haɗa da auren mace fiye da ɗaya, wayar salula da kuma adashi.

Ƙungiyar wadda ke da alhakin sasanta rigingimun ma’aurata ta ce a shekarar da ta wuce ta 2024, ta raba aure 1,433 a birnin Yamai.

Haka kuma a rahoton da ta fitar ƙungiyar ta ce ta yi nasarar sulhunta aure 2,565.

Rawar da wayar salula ke takawa

Isa Karimu wani ɗan jamhuriyar Nijar ya ce ya kamata malamai su ƙara ƙoƙari su yi wa’azi wajen nusar da jama’a cewa aure ibada ne sannan a lura da irin rikicin da wayar salula ke haɗawa.

“Ni kaina idan na shiga gidana to zan ajiye waya ne sai kuma idan zan fita. Saboda da zarar waya ta yi ƙilin to dole ne hankalin maiɗakinka ya je wurin kamar yadda kai ma idan ka ji ƙarar wayarta hankalinka zai koma.”

“Ya kamata malamai a masallatan Juma’a a rinƙa wa’azi domin janyo hankalin maza da mata dangane da zamantakewar aure.”

‘Akwai auren da ya mutu ranar da aka ɗaura shi’

“Akwai auren da wallahi ranar da aka ɗaura shi amaryar ba ta kwana a gidan mijinta ba. Cikin dare ya ɗauko ta ya kai ta ƙofar gidansu ta shiga shi kuma ya wuce”, in ji Nana Hadiza, wata ƴar gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan’adam a Yamai.

Nana Hadiza ta ce laifin na dukkannin ɓangarorin biyu ne duk da dai rashin sanin haƙƙin mata na taka gagarumar rawa.

“Ba a san darajar macen ba. Ba a san haƙƙokin macen ba. Kuma ita kanta macen ba ta san darajar aurenta ba. Ba ta san kuma haƙƙoƙin da Allah ya ɗora mata ba da na mijinta a kanta a cikin zamantakewarsu ta aure.”

“To a haka nan za ka ga aurarrakin da za a yi su sun zo ba yadda ake tsammani ba.”

Rawar da ci-rani ke takawa

A jamhuriyar Nijar, waɗansu mata da mazajensu ke zaune a ƙasar waje da sunan ci-rani na kokawa saboda rashin komawar mazajen nasu gida a kan lokaci, lamarin da ke haifar da mutuwar aure a lokuta da dama.

Akasarin matan da BBC ta tattauna da su sun ce mazajen nasu sun kwashe shekara-da-shekaru a ƙasashen waje ba tare da dawowa ba.

Hajiya Aisha, wadda ba sunanta kenan ba na cikin matan da BBC ta yi hira da su; ta ce mijinta ya tafi Amurka shekaru goma sha biyar da suka gabata amma har yanzu bai dawo ba.

A cewarta, “Tun da ya tafi Amurka shekaru 15 da suka wuce bai dawo ba, har na gaji da zama amma iyayena sun ƙi yarda a kashe aure na da shi.”

Matan sun ce duk da yake mazajen na aiko musu da kuɗin kashewa, ba sa gamsuwa idan ba mazajen ne suka dawo ba.

By Ibrahim