Wakilin Amurka na musamman Amos Hochstein ya isa birnin Beruit a ranar Litinin don tattaunawa da nufin samar da mafita kan rikicin da ke kan iyakar Isira’ila da Lebanon.

Wannan wani bangare ne na yunkurin diflomasiyya, wanda kuma ya kai Sakataran Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken zuwa yankin domin neman tsagaita wuta a Zirin Gaza.

Hochstein ya shaida wa manema labarai ya yi wata ganawa mai ma’ana tare da Nabih Berri, Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon, kuma a lokacin da yake Lebanon zai tattauna da mambobin gwamnati, da sojoji da duk wani wanda ke son yin aiki a kan sanya kasar kan sabon tsari na karfi, tsaro, kwanciyar hankali da kuma wadatar tattalin arziki.

Wakilin na Amurka na musamman ya kuma yi tsokaci kan Kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701, wanda aka amince da shi a karshen yakin da ya wuce tsakanin Isira’ila da Hezbollah a 2006, wanda har ila yau ya hada da kira ga Hezbollah ta janye mayakanta da ke arewacin Kogin Litani na kasar Lebanon, sannan Isra’ila ta janye sojojinta daga Lebanon.

Hochstein ya ce, mutanen Lebanon kamar kowa a yankin, na bukatar komawa gida ne kawai, tare da gina ingantacciyar makoma cikin kwanciyar hankali da ci gaban kansu da iyalan su.

A ranar Litinin ake sa ran Blinken ya isa yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda ma’aikatar harkokin waje ta sanar cikin wata sanarwa.

By Ibrahim