A ranar Juma’a shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya nada wani na hannun daman shi cikin majalisar zartaswa, wanda shugaban Amurka Joe Biden yayiwa afuwa a bara, a wani musayar bursunoni, biyo bayan tabbacin cewa, Venezuela zata gudanar da ingantaccen zabe a shekarar 2024.

Maduro ya nada Alex Saab ministan masana’antu da sarrafa kayayyaki a cikin gida, inda ya dora mishi alhakin ciyar da tsarin masana’ntu a Venezuela gaba, bisa tsarin jadawalin da aka tsara na abinda ya kira ‘Sabon salon tattalin arziki’. Maduro ya sanar da hakan ne ta kafar sadarwar Telegram.

Saab ya dawo Venezuela a matsayin mai yanci a watan Disamba, bayan kasancewa a tsare tun shekarar 2020, lokacin da jami’ai a Cape Verde suka kama shi bisa umurnin Amurka kan laifin safarar kudi, wanda masu gabatar da kara a Amurka ke mishi lakabi da dan koren Maduro.

Shugaba Maduro ya samu sako shi, da yi masa afuwa a wata yarjejeniya da aka cimmawa da gwamnatin Biden. A musayar data ceto Saab, Maduro ya saki Amurkawa 10 da wani da shari’a ke nema, Fat Leonard, wanda ake nema bisa zargin da ake masa na taka rawa a wata gagarumar badakalar cin hanci a Pentagon.

Sakin bursunonin Amurka mafi girma a tarihin Venezuela ya faru ne makonni bayan da fadar white House ta sakarwa kasar dake kudancin Amurka mara, a takunkuman tattalin arziki da ta zarga mata, biyo bayan tabbacin da Maduro ya bayar na yin aiki tare da abokan adawar siyasa domin ganin an gudanar da ingantaccen zaben shugaban kasar na shekarar 2024.

Amurka dai ta janye sassaucin takunkuman a farkon shekarar nan, bayan dishewar gurin ta na ganin an samu budi ga demokradiyya.

A watan jiya Amurkan ta maida wani martani ga zaben shugaban kasar ta Venezuela na watan Yuli mai cike da takadda, ta sanya takunkumi ga kawayen Maduro su 16, inda aka zarge su da yin kafar angulu ga zabe, da gudanar da aiyukan cin zarafin bil’adama.

A shekarar 2020 ne aka kama Saab a yayin da jirgin da yake ciki ya tsaya shan mai a kan hanyar shi ta zuwa Iran, domin gyaro wata yarjejeniya kan man fetur a madadin gwamnatin Maduro. Laifuffukan da Amurka ta zarge shi da su, sun hada da hada baki domin safarar kudi dake da alaka da wani salon cin hanci da akai zargin ya kunshi zunzurutun kudi dalar Amurka milyan 350, ta hanyar gwangilar gina gidaje masu saukin kudi a kasar.

By Ibrahim