Masana tattalin arziki sun ce hanyoyi biyu mafiya inganci wajen tura kudi a harkar cinikayyar kasa da kasa su ne ta takardun tabbaci na LC da TCC daga bankunan bangarorin biyu dake huldar kasuwanci da juna, kuma matakin da bankin CBN ya dauka a kan wannan salon damfara na SWIFT ya zo daidai da gaba.
Matakin da babban bankin Najeriya ya dauka dai na zuwa ne a daidai lokacin da salon damfara da sunan tsarin biyan kudi tsakanin abokan huldar kasuwanci ke kara kamari inda ‘yan kasuwa da basu ji ba su gani ba a ciki da wajen Najeriya ke rasa dukiyarsu ga wannan tsari na karya kuma hakan ke zama sanadiyar karayar tattalin arzikin wasu har abada.
A akasarin lokuta dai ana amfani da takardun bogi kamar SWIFT MT103, SWIFT Ack copy, da dai sauransu wajen yaudara ‘yan kasuwa a sunan an biya su su saki kayayyakin su, daga bisani bayan tura kaya ba’a ga kudi ba wadanda al’amarin ya shafa su garzaya zuwa CBN don mika korafi.
Badakalar musayar kudade tsakanin ‘yan kasuwan kasa da kasa na SWIFT Code dai abu ne da ke kara tsananta musamman a cikin watannin baya-bayan nan inda hakan ya zama silar rasa rayukan wasu ‘yan kasuwa da suka rasa dukiyarsu ga wannan hanyar kamar yadda wasu alkaluma daga yanar gizo suka yi nuni.
Duk kokarin ji ta bakin bankin CBN a kan yadda zai aiwatar da tsarin hada wadanda irin wannan al’amari zai shafa daga yanzu ga jami’an tsaro don daukan matakan da suka dace ta kiran wayar tarho da sakon kar ta kwana dai ya ci tura a yayin hada wannan rahoton.
Saurari cikakken rahoton: