Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fayyace yadda zai aiwatar da janye tallafin man fetur da kawo sauye-sauye a kasuwar musayar kudaden kasar.

A ranar da aka rantsar da shi Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana kawo karshen biyan tallafi a kan man fetur. Inda masu suka a kan al’amura suka ga baiken dukkanin manufofin 2 wadanda suka ce sun sabbaba tsananin rayuwa a kasar.

Sai dai, Atiku, wanda ya kasance daya daga cikin masu sukar kuma ya yi rashin nasar a hannun Tinubu a zaben shugaban Najeriya na 2023 , ya bada bayanin yadda zai aiwatar da manufofin 2 idan da an zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.

A cikin wani dogon sakon daya wallafa a shafinsa na X a jiya Lahadi, dan takarar shugaban kasar karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasar daya gabata ya wallafa cewar zai fara ne da magance matsalar cin hanci da rashawa a matsayin wani bangare na manufarsa akan batun janye tallafin man fetur.

“Da fari, magance almundahana. kamata ya yi a fara da dakile almunadahana ta hanyar yiwa kamfanin NNPCL, wanda yafi kowa cin gajiyar halin da ake ciki garanbawul. Akwai tuhuma a kan jajircewarsa wajen aiwatar da sauye-sauye da kuma iyawarsa wajen aiwatarwa da tabbatar da sun yi aiki,” a cewar Atiku.

“Batun tallafin man ya samar da kafar yin almundahana, kuma sauye-sauyen na yiwa NNPCL da iyayen gidansa barazana.”

Game da batun sauye-sauye a kan musayar kudade kuma, tsohon mataimakin shugaban kasar yace sakin Naira ba tare da kaidi ba mataki ne da ya zarta ka’ida.”

Atiku yace, a maimakon hakan shi zai karfafa gwiwar babban bankin Najeriya ya bullo da matakin bin abu daki-daki a harkar musayar kudaden. Yace za’a fi kaunar tsarin sakin kaidin sannu a hankali.”

Sai dai a cikin wani martanin gaggawa, fadar shugaban kasar ta soki sauye-sauyen da tsohon mataimakin kasa Atiku Abubakar ya gabatar, inda ta bayyanasu da “dokin mai baki”.

“Da fari dai, ‘yan Najeriya dai sun yi fatali da wannan tunani na Alhaji Atiku, da suka bayyana da maras hikima a zaben 2023. Idan da ya samu nasara a zaben, mun yi imanin cewa da sai ya jefa najeriya a yanayin da dara wanda ake ciki muni ko kuma ya gudanar da gwamnatin tuwo na mai na”, kakakin shugaban Najeriya Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a sanarwar daya wallafa a shafinsa na X.

“Wasu daga cikin dalilan da suka sabbabawa Atiku faduwa a zaben sun hada da shan alwashin cefanar da kamfanin nnpcl da kadarorinsa ga abokansa. ‘Yan Najeriya basu manta da wannan ba, kuma hankulansu ba zasu kwanta da sanin tarihin yadda Atiku ya gudanar da tattalin arziki a zangon farko na gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo tsakanin 1999 da 2003.

“Zance abu ne mai sauki. Babu wahala ga magori ya wasa kansa da kansa tare da sukar manufofin abokan hamayyarsa koda kuwa akwai alkaluman dake nuni da cewar sauye-sauyen tattalin arzikin na samarda da mai idanu duk da ‘yan wahalhalun da za’a sha na wucin gadi.

“A matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kula da wani shirin cefanar da kadarorin gwamnati mai cike da tuhuma. Shi da uban gidansa sun nuna rashin gamsuwarsu da tsarin ilminmu, inda dukkaninsu 2 suka kafa jami’o’insu tare da kyale namu suna fama.

By Ibrahim