Sakamakon wannan zaben, kasancewar Amurka babbar abokiyar kawance ce ga Ghana ta fannoni daban-daban da suka hada da kasuwanci, zuba hannun jari, da tsaro zai yi tasiri ga kasar sosai, tun da dangantakar tattalin arziki tsakanin Ghana da Amurka na da fadin gaske.
Ghana na cin gajiyar tsarin kasuwanci tsakanin Afirka da Amurka na AGOA, wacce ke ba da damar shiga kasuwannin Amurka ba tare da haraji ba ga wasu kayayyakin Afirka.
Har ila yau, Amurka na daya daga cikin manyan abokan huldar kasuwanci na Ghana, inda cinikayyar kasashen biyu ya haura sama da dala biliyan 2 a shekarar 2022.
Sai dai duk da haka, masanin tattalin arzikin kasa, Hamza Attijjany ya ce, Ghana ba ta ji wasu manufofin da za su ci gaba da taimakawa tattalin arzikinta daga ‘yan takaran biyu ba.
“Idan muka lura da kamfen da Kamala Harris da Donald Trump suke yi, ba mu ji sun fito da wani kuduri mai kyau da cewa idan sun lashe zabe ga gudunmawa da za su ba Afirka… don haka ne mutanen Ghana ba su sa ido sosai a wannan zaben kamar yadda aka saba a da ba”.
Ghana na da dumbin ‘yan asalin kasar da ke zaune a Amurka, wadanda sakamakon zaben zai shafi rayuwarsu.
Haka kuma batun amincewa da auren jinsi ke da muhimmanci. Babban Sakataren jam’iyar CPP na yankin Ashanti, kuma masani ka hulda tsakanin kasa da kasa, Issah AbdulSalam ya ce;
“Da Kamala Harris ta zo Ghana, ta gaya mana cewa mu bai wa kowa (‘yan luwadi da madigo) dama su yi abin da suke so, in dai wannan abin bai take dokar Ghana ba, saboda haka, za su matsawa Ghana su bi kudurin (auren jinsi) don suna taimakawa Ghana kwarai a fannin tattalin arziki”.
Malam Issah ya kara da cewa, idan jam’iyar Donald Trump ce ta yi nasara a zabe, rayuwar ‘yan Ghana da sauran ‘yan Afirka da ke zaune Amurka za ta samu matsala domin manufarsa game da bakin haure.
Ghana, kamar sauran kasashen Afirka, na kallon zaben da burin ganin yadda Amurka za ta yi hulda da Afirka a karkashin sabuwar gwamnati. Batutuwa irin su kasuwanci, tsaro, da taimakon raya kasa na da matukar muhimmanci.
Irbard Ibrahim, masani ne kan tsaro da hulda tsakanin kasa da kasa ya ce yadda kasar Sin da Rasha ke walwala a Burkina Faso, Nijr da Mali, idan Donald Trump ya yi nasara a zaben, zai iya rage tasirin da suke da shi a kasashen, amma Kamala Harris, “Jam’iyarta, watakila za ta sasanta da China a bangaren kasuwanci da sauransu.”
Hakika, ana sa ido sosai kan zaben Amurka a Ghana saboda gagarumin alakar tattalin arziki, tsaro, da diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.
Sakamakon zaben zai yi tasiri ga harkokin kasuwanci, tsaro, da rayuwar al’ummarta da ke zaune a Amurka.
Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah: