Kamfanin hakar ma’adinai na Zijin na kasar China ya shirya tsaf don sayen aikin hakar gwal a mahakar ma’adinai na Akyem da ke Ghana daga kamfanin Newmont na kasar Amurka a kan dala biliyan daya.

Ana sa ran kammala yarjejeniyar a karshen rubu’in shekarar 2024, wanda ya kunshi tsabar kudi dala miliyan 900, da kuma karin dala miliyan 100 bayan an cika wasu sharudda.

Shin za a iya kallon wannan, a matsayin wani bangare na kara fadada aniyar tabbatar da kasancewar kasar China a Afirka? Wakilin Muryar Amurka Idris Abdullah Bako ya tattauna da masanin tattalin arziki da wasu masu ruwa da tsaki kan wannan sabuwar yarjejeniya.

Kamfanin Newmont na kasar Amurka ya yanke shawarar sayar da mahakar ma’adinai na Akyem ga kamfanin Zijin, mafi girman kamfanin hakar ma’adinai na kasar China, domin cimma wani bangare na ci gaba da shirin karkatar da kadarori zuwa ga ma su hannun jarin kamfanin, kamar yadda shugaban Newmont, Tom Palmer ya fada a wata sanarwa da kamfanin ya fitar kan yarjejeniyar.

Mista Palmer ya kara da cewa, ‘Kammala wannan yarjejeniya cikin nasara zai kara karfafa amincewarmu ga Ghana, a matsayin mafi dacewar wurin hakar ma’adinai’.

Idan muka yi la’akari da cewa, da cewa wadannan kamfanuka biyu, na kasashe ne dake gogayya da juna don samun gindin zama da fada a ji, a nan Afirka, wato kasar Amurka da China. Sai dai in ji masanin tattalin arziki da harkokin kudi, Hamza Attijany, kasar Amurka da China na da huldar kasuwanci mai kyau, wanda ya yi tasiri ga wannan yarjejeniyar. ‘Dalilin da ya sa Newmont ta sayarwa Zijin aikin hakar ma’adinai na Akyem shi ne: farko, tana bukatar makudan kudade don ci gaba da harkokinta na yau da kullum, sannan lokaci ya kai da a maidawa wadanda suka zuba hannun jari a kamfanin kudadensu’ In ji shi.

Irbard Ibrahim, masani ne a kan tsaro da hulda tsakanin kasa da kasa, yace duk da cewa Amurka na da karfin soji da tattalin arziki, amma kasar China na kara fadada tushen tabbatar da kanta a Ghana da Afirka baki daya. Yace,China ba ta fi Amurka fada a ji ba a nan Afirka, amma tasirinta na kara fadada, don haka ya kamata kungiyoyin farar hula su matsawa gwamnati lamba yadda za ta tabbatar Ghana ta samu amfanin wannan yarjejeniyar hakar ma’adinai daga kamfanin Zijin.

Kungiyoyin farar hula da masana sun yi suka ga wannan yarjejeniyar kasuwanci, inda suka ce za ta kasance nasara ga wadannan kamfanuka biyu, Newmont da Zijin, amma banda Ghana.

Shugaban Asusun Zuba Jari kan Ma’adinai (MIIF), Farfesa Douglas Boateng, yace wannan cinikin cin fuska ne ga Ghana, domin da ya kamata a tuntubi asusun kafin a kai tayi ga kamfanin China.

Alhaji Baba Ahmed, mai tsara shirye-shirye ne na kungiyar kananan masu hakar ma’adinai dake da lasisi, da yake tsokaci yace idan wani abu makamancin wannan yarjejeniyar ya taso, ba a gayyatar kamfanukan hakar ma’adinai na Ghana, kuma a cikinsu akwai wadanda, idan sun yi hadin gwiwa, za su iya sayan aikin hakar ma’adinai na Akyem.

Kamfanin Newmont dai, ya ce zai ci gaba da aiki a Ghana, ciki har da zuba jarin dala miliyan 950 zuwa dala miliyan 1,050 a aikin hakar zinare a arewacin Ahafo dake yankin Ahafo na Ghana.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako daga Accra:

By Ibrahim