Jita-jita game da mutuwar shugaban kasar Paul Biya mai shekaru 91 da haifuwa, ta kaure bayan ya bace a idon jama’a sama da wata guda bayan wata ziyarar aiki da ya kai kasar China.

Gidan rediyon kasar Kamaru ya ce shugaban kasar Paul Biya da wasu masu ba shi shawara da mai dakinsa Chantal Biya, sun koma birnin Yaounde bayan shafe kusan kwanaki 50 a wajen kasar da ke yammacin Afirka.

An kuma watsa da dawowar Biya kai tsaye ta gidan talabijin na kasar, wanda ya nuna dubban mutane ne suka taru a manyan mahadar da ke kusa da filin jirgin saman Yaounde Nsimalen, inda Biya ya sauka.

Malami mai shekaru talatin da biyar a fannin ilmin sinadarai Mbang Boniface, na daga cikin jiga-jigan farar hula, wadanda da yawa daga cikinsu sun damu da rashin ganinsa.

Ya ce ya yi mamakin yadda gwamnatin Kamaru ta ba da muhimmanci sosai ga dawowar Biya ba tare da fadawa farar hula inda shugaban yake ba.

Ya ce, “An wayi gari da safe da ganin wannan gagarumin taron ma’aikata da dalibai, domin tarbar wani wanda ba mu san inda yake ba, kuma hakan ba kawai ya rage ayyukan tattalin arziki ba ne, har ma ya dakatar da ayyuka. ‘Yan kasar sun damu idan shugaban da zai shigo yana cikin koshin lafiya ko a’a. Abin kunya ne.”

Fararen hula sun ce akwai dimbin sojoji a babban birnin Kamaru lokacin da Biya ya isa. Rundunar sojin ta ce an tura dakarun gwamnati ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yayin da sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa ke kare Biya da kansu, kamar yadda al’ada ta tanada.

Daruruwan Hotunan Biya masu dauke da sakonnin barka da dawowa gida an gansu a mahadar tituna.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya kan hanyarsa ta zuwa fadarsa.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya kan hanyarsa ta zuwa fadarsa.

Magoya bayan jam’iyyar adawa ta Kamaru ko kuma CPNR, sun fito suna rera taken gaya wa Biya cewa ya tsufa kuma ya mika mulki.

Biya mai shekaru 92 ya kasance shugaban kasar Kamaru fiye da shekaru arba’in.

A ranar 4 ga watan Satumba ne ya bar yankin tsakiyar Afirka don halartar taron dandalin tattaunawa tsakanin China da Afirka.

Bayan ya bar China a ranar 8 ga Satumba, sama da wata guda ba a gan shi a bainar jama’a ba, abin da ya haifar da jita-jita a cikin rahotannin labarai da shafukan sada zumunta cewa watakila ya mutu.

A lokacin, gwamnatin Kamaru ta ce Biya na cikin koshin lafiya kuma yana aiki don ci gaban kasar a Geneva. Gwamnati ta ce jirginsa ya tashi daga Geneva zuwa Yaounde ranar Litinin.

By Ibrahim