Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa Burtaniya a yau Laraba domin fara hutun makonni 2 a wani bangare na hutunsa na shekara.

Sanarwar da mataimakinsa na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a yau tace Tinubu zai yi amfani da makonni 2 ne a matsayin hutun dake hade da aiki domin sake nazarin sauye-sauyen gwamnatinsa akan tattalin arziki.

Tinubu da Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume

Tinubu da Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume

Zai dawo gida Najeriya bayan karewar hutun nasa.

Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike

Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike

Shugaba Tinubu ya gudanar da bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya na 64 ta hanyar gabatar da jawabi, inda ya shaida cewar gwamnatin tarayya na shirin bijiro da wani taron kasa na kwanaki 30 da nufin shigar da matasa cikin gwamnatinsa.

Tinubu da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle (hagu) da Mai baowa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu (dama)

Tinubu da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle (hagu) da Mai baowa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu (dama)

Ya kara da cewar nan bada jimawa ba za a fito da tsare-tsaren taron da kuma hanyoyin da za a zabo wakilan da zasu halarce shi.

By Ibrahim