A yayin da duniya ke karkata ga tsarin tsaftattaccen makamashi sakamakon kiraye-kirayen kwararru a fannin, gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ma’aikatar Albarkatun Man Fetur tare da hadin gwiwar Gidauniyar FOSSREA mai rajin neman dorewar tallafin kamfanoni ga al’umma ta Afrika za ta karbi bakuncin taron kasa da kasa na makamashin hydrogen na farko, daga ranar Talata 26 zuwa Alhamis 28 ga watan Nuwambar bana, a dakin taron fadar shugaban kasa, Aso Villa.
An tsara gagarumin taron mai taken “Gina tattalin arzikin hydrogen ga Najeriya” da zimmar inganta albarkatun hydrogen a matsayin tushen samar da makamashi mai tsafta mai dimbin yawa don rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, inganta makamashi, samar da ayyukan yi da kuma bunkasa ci gaban tattalin arziki a dai dai lokacin da kasashen duniya ke gangamin komawa ga tsarin tsaftataccen makamashi.
Tuni dai Masana da masu fafutukar ganin Najeriya ta karkata zuwa ga fannin tsaftattacen makamashi suka fara cewa taron makamashi na hydrocarbon da zai hada kan masu zuba jari na cikin gida da wajen zai taimaka wa kaşar samun karin kudadden shiga.
Jagoran tsare-tsaren kungiyar Connected Development, Mukhtar Modibbo, ya ce, lokaci ya yi da kasashen Afrika zasu tashi tsaye ga harkar tsaftataccen makamashi don kawo sauki ga gurbatar yanayi ta hanyar amfani da man fetur baya ga samun damar kudadden shiga.
Ita ma mai waken baka, Maryam Bukar Hassan wacce aka fi sani da Alhan Islam, ta sha yin kira ga ‘yan Najeriya su bada karfi ga fannin tsaftataccen makamashi don kawo Sauki ga matsalar sauyin yanayi.
Taron zai samu halartar mutane sama da dubu 1 da suka hada da masu baje kolin hajarsu, masu zuba jari daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su daga kasashen Afirka, Turai, Asiya, da Amurka wanda aka yi imanin cewa taron zai samar da hadin gwiwa wajen tsarawa da kuma tabbatar da makomar tsarin samar da makamashi a Najeriya.
A yayin taron, tattaunawar za ta mayar da hankali kan batutuwa masu mahimmanci ciki har da samar da makamashin hydrogen, damar zuba jari, ci gaban harkar rarraba makamashi, tsare-tsaren manufofin; magana a kan ilimin fasaha, haɓaka ababen more rayuwa da bude hayoyin hydrogen da Najeriya za ta sami kudadden shiga a fannin makamashin hydrogen.
Ana kuma sa ran taron zai kawo wani gagarumin sauyi a fannin makamashi a Najeriya.