An nada tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar Chelsea da kasar Ingila Frank Lampard ya zamo kociyan Coventry a bisa yarjejeniyar shekaru 2 da rabi, a cewar kungiyar.

Lampard ya maye gurbin Mark Robins, wanda aka sallama a farkon wannan watan.

Coventry na mataki na 17 a gasar zakarun bayan wasanni 17 inda suka yi rashin nasara a wasanninsu 4 na karshe.

A matsayinsa na dan wasa, Lampard ya ciwa Chelsea kwallaye 211 a dukkanin gasar da ta buga a shekaru 13 da ya shafe a cikinta masu cike da daukar kofi.

Ya taba horas da kungiyoyin Chelsea da Everton a gasar firimiya, haka kuma ya horas da kungiyar Derby County.

Lampard zai karbi ragamar horas da Coventry a karon farko ran Asabar mai zuwa inda za ta kara da kungiyar Cardiff City a filin wasa na Coventry Building Society.

By Ibrahim