Ya kuma sauyawa 10 wurin aiki sannan ya mika sunayen sabbin ministoci 7 din da zai nada ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.

Shugaban kasar ya sallami ministar harkokin mata, Uju-Ken Ohanenye da ta yawon bude ido; Lola Ade-John da ministan ilimi, Tahir Mamman da karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo da kuma Jamila Ibrahim, ministar ci gaban matasa.

Tinubu ya mika sunan Bianca Odumegu-Ojukwu a matsayin karamar ministar harkokin waje sannan ya mika sunan Nantawe Yilwatda a matsayin ministar bada agaji da rage talauci, inda ya kawo karshen wa’adin dakatacciyar minista Betta Edu a hukumance.

Haka kuma shugaban kasar ya mika sunan Maigari Dingyadi, a matsayin ministan harkokin kwadago da ayyukan yi da Jumoke Oduwole a matsayin ministar masana’antu da Idi Maiha a matsayin ministan sabuwar ma’aikatar da aka kirkira ta bunkasa kiwon dabbobi, da Yusuf Ata a matsayin karamin ministan gidaje da raya birane, da Suwaiba Ahmad a matsayin karamar ministar ilimi.

An yanke shawarar ne a zaman majalisar zartarwa ta tarayya na yau Laraba a Abuja, kamar yadda aka wallafa a shafin x na mashawarcin shugaban kasa na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga.

Yanzu an kirkiri ma’aikatar kula da cigaban yankuna da zata rika sa idanu akan ayyukan hukumomin kula da yankuna irinsu na neja delta dana arewa maso yamma dana kudu maso yamma da kuma na arewa maso gabas.

Hukumar kula da harkokin wasanni ta kasa zata karbe ayyukan ma’aikatar wasanni.

Majalisar zaetarwar ta kuma amince da hade ma’aikatar yawan bude idanu data al’adu da kirkire-kirkire a wuri guda.

Duk da wannan sanarwa, Onanuga bai bayyana abin da zai faru da ministocin dake rike da ma’aikatun da aka rushe ba ko kuma yadda ayyukansu za su kasance a nan gaba.

Abubakar Momoh ne ke rike da ma’akatar cigaban yankin neja delta, inda John Enoh ke jagorantar ma’aikatar wasanni.

By Ibrahim