Kociyan riko na tawagar kwallon kafar Najeriya “Super Eagles”, Augustine Eguavoen, ya gayyaci ‘yan wasa 23 domin fafatawar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da zasu yi da jamhuriyar Benin da kasar Rwanda.
Cikin ‘yan wasan da aka tsara zasu taka rawa a fafatawar har da dan wasan gaban kungiyar Galatasaray, Victor Osimhen, wanda ya kasance baya nan a wasan da tawagar ta kara da Libya saboda rauni.
Bayan dawowar daga jinya ne ya ciwa Galatasaray daya daga cikin kwallaye 3 a wasan data buga a gidan kungiyar Antalyaspor a gasar lig ta kasar Turkiya a ranar 19 ga watan Oktoban daya gabata.
Osimhen ya kuma zura kwallon data baiwa Galatasaray nasara a fafatawar kece raini tsakaninta da Besiktas a ranar 28 ga watan Oktoban da ya gabata.
Har ila yau, ‘yan wasan da zasu dawo tawagar ta Super Eacles bayan sun jima basa nan harda Umar Sadiq na Real Sociedad.
Wasannin da za’a buga da Jamhuriyar Benin da Rwanda zasu kasance na zagayen karshe na gasar ta afcon da zata gudana a kasar Morocco a badi.
Fafatawar rana ta 5 da za’a yi da Jamhuriyar Benin a filin wasa na Felix Houphouet Boigny zata gudana ne a ranar 14 ga watan Nuwamba da misalin karfe din dare agogon Najeriya, yayin da fafatawar rana ta 6 da kasar rwanda zata gudana a filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo a ranar 18 ga watan Nuwambar da muke ciki.
Yanzu daya kasance da sauran wasanni 2, Najeriya ce kan gaba a rukunin D da maki 10 bayan da hukumar kwallon kafar Afrika (CAF) ta bata kyautar maki 3 saboda kwantan wasa tsakaninta da Libya.
Ga jerin ‘yan wasa da Eguavoen ya gayyata: