Tsohon dan wasan United Ruud van Nistelrooy, wanda ya karbi ragamar aiki na wucin gadi bayan an kori Erik Ten Hag a ranar Litinin, zai ci gaba da aiki har a buga wasanni uku masu zuwa.
Amorim shi ne koci na shida na dindindin da United ta nada tun bayan da aikin Sir Alex Ferguson na shekaru 26 ya kare kana ya yi ritaya a 2013.
A cikin wata sanarwa, kulob din ya ce “Ruben yana daya daga cikin matasa masu horar da ‘yan wasa da aikin su ke kayatarwa kuma masu daraja sosai a wasan kwallon kafa na Turai”.
A farkon makon, Sporting ta ce United ta amince ta biya Yuro miliyan 10 (£ 8.3m) don dauko batun sakin Amorim.
Wasan farko da Amorim zai yi a Manchester United zai kasance ne ranar 24 ga Nuwamba da sabuwar kungiyar Ipswich, wanda ke zuwa bayan hutun kasa da kasa.
Wasansa na farko a gida zai buga da kungiyar Bodo/Glimt ta kasar Norway a gasar cin kofin Europa ranar 28 ga watan Nuwamba, tare da wasan Premier da Everton.